Labarai

Har yau nasarorin Buhari ba su kusa kai nawa ba – Jonathan

Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, ya bayyyana cewa har yau nasarorin wannan gwamnati mai mulki ba su ko kama kafar nasarorin gwamnatin sa ba.
Jonathan ya bayyana haka ne ta bakin kakakin yada labaran sa, Ikechukwu Eze, a yau Juma’a, ya na mai cewa sukar da gwamnan jihar Borno ya yi wa gwamnatin sa cewa ba tagari ba ce, ba komai ba ne sai ‘hauragiya da rashin kaifin tunani.”
Tsohon shugaban kasar ya yi wannan martani ne ga jawabin da gwamnan Barno, Kashim Shettima ya yi a wurin kaddaqmar da littafin da Bolaji Abdullahi, kakakin yada labaran jam’iyyar APC, ya rubuta, wanda aka kaddamar jiya Alhamis, a Abuja.
Jonathan ya ce lokaci ya yi da gwamnan Barno zai fito flli ya fada wa duniya rawar da ya taka wajen sace ‘yan matan Chibok.
“Sai Kashim Shettima ya fito yanzu ya fada mana idan Jonathan ne ya sa shi tura daliban Chibok makaranta su yi jarabawa, alhali gwamnatin tarayya ta bada dokar cewa kada jihohin nan uku, Barno, Yobe da Adamawa su sake su kai dalibai su zauna jarabawar WAEC a yankunan da babu tsaro.”
Littafin dai ya na kunshe ne da labarin yadda Jonathan ya ci nasara zama shugaban kasa da kuma yadda ya yi sakacin da ya kai shi ga faduwa zabe.
Jonathan ya bayyana littafin da cewa kundin soki-burutsu ne kawai.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button