Kanywood Maja Sun Ziyarci Ganduje A Fadar Gwamnatin Kano (Hotuna)
Tun da farko jarumi Mustapha Naburaska ne ya wallafa sanarwar ziyarar tare da hotunan jaruman a shafinsa na Instagram, inda a cikin ɗaya daga cikin hotunan an ga yadda gwamna Abdullahi Umar Ganduje ke dafa kan shahararren Fardusa na fina-finan Hausa, Alhaji Hamisu Lamido Iyantama.
Idan za a iya tunawa dai a cikin watan Satumbar da ya gabata ne Jarumi Mustapha Naburaska ya ce ya ajiye Jar Hularsa Saboda ba gadar ta ya yi ba. Inda ya ce yanzu ya rungumi tafiyar Ganduje ka’in da na’in saboda a cewar sa ban da jihar Lagos babu inda ake zuba aiki kamar jihar Kano.
Jaridar labarai24 ta kara da cewa Sauran jaruman da su kai ziyarar fadar gwamnatin Kano sun haɗa Sulaiman Bosho da Kabiru Maikaba da Shehu Hassan Kano da Hajara Usman da Hadizan Saima da sauran fitattun jarumai a masana’antar ta Kanywood.
A shekarun baya dai ba kasafai ake ganin jaruman na Kannywood suna fitowa su nuna alkibilarsu a siyasance ba, amma a baya-baya nan lamarin ya sauya.
Akan gan su sun yi kwamba suna kai wa ‘yan takara ziyara, su kuma hada kai su yi masu wakoki daban-daban, abinda kan haifar da rarrabuwar kawuna a tsakaninsu.