KannywoodUncategorized

Don Fadarkwa Muke Harka Fim – Rukayya Dawayya

Rukayya Umar Santa, wacce aka fi sani da Rukayya Dawayya. Ta yi kira ga Jama’a da su rinka yi wa yan fim kallo ya’yan da iyayen su ka yi aure suka haife su iyaye su, kuma suka ba su tarbiyya suka saka su a makaranta. ”
Don Fadarkwa  Muke Harka  Fim  - Rukayya Dawayya
Jarumar ta bayyana hakan ne ga wakilin jaridar Dimukaradiyya a lokacin tattaunawar su da ita.

Ta Kara da cewar” Duk abin da aka ga muna yi, ba muna yi ba ne don mu bata tarbiyyar wani, don haka muna kokarin fadakar da Jama’a ne, domin su fahimci yadda rayuwar duniya take. ”

Ta ci gaba da cewa” Ni dai na dauki fim a matsayin harkar Sana’a kamar yadda kowacce mace za ta fito ta tafi aikin Office ko kasuwancin ta, to haka mu ma mu ke daukar fim.” Inji ta.

“Don haka duk in da aka gan mu aiki mu ke yi, kamar sauran mata da su ke yin aiki. Mu kan sa a ran mu mun tafi aikin mu na neman Halak ne, don haka sai a rinka yi mana addu’a a rinka yi mana kallo na adalci. ” a cewar ta.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button