Labarai

Anyi Mata Auren Dole Ta Kashe Mijinta Sati Ukku Da Aure

Sunanta Rumasa’u Muhammad tana da zama a garin Wuro Yanka karamar hukumar Shelleng jihar Adamawa, shekarunta 19
An daura mata auren dole da wani mutumi wanda bata so mai suna Muhammad Adamu dan shekara 35, ta nemi mijin ya saketa amma yaki, tabi duk hanyar da ya kamata ya saketa amma yaki, shine sai tayi amfani da wuka yana bacci ta burma masa a cikinsa
Datti Assalafy ne ya ruwaito labarin. Kafin a garzaya dashi Asibiti ya mutu, ‘yan sandan Shelleng sun kama matar, binciken farko na ‘yan sanda ya tabbatar da cewa an mata auren dole ne a ranar 6-8-2021, sati uku da yin auren ta kashe mijin
Maigirma Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Adamawa CP Aliyu Adamu Alhaji ya bada umarni a gudanar da cikakken bincike a gurfanar da ita a kotu don ta fuskanci hukunci, sannan ya bada shawara wa al’umma su guji yin auren dole

Anyi Mata Auren Dole Ta Kashe Mijinta Sati Ukku Da Aure
Anyi Mata Auren Dole Ta Kashe Mijinta Sati Ukku Da Aure

Ni kam a fahimtata babu dakikin mutum namiji kamar wanda ya nace akan sai ya auri matar da bata son shi, wannan wauta ne, kuma karshen abinda yake faruwa kenan ta kashe ka
Yawanci iyayen yarinya idan makwadaita ne suna bada gudunmawa sosai wajen yiwa yaransu mata auren dole ga masu arziki
Maza ku guji auren dole, babu dadi sam ka auri wacce bata sonka, ga mata nan birjik a gari sai wanda ka zaba, me zai kai ka ga auren dole imba wauta ba?
Allah Ya sauwake

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button