Uncategorized

ILLolin Madigo Ga Al’umma

Ba wani abu bane wannan face yawaitawar samuwar mata ‘yan madigo.
Dole a kira wannan abin da masifa domin yana daga cikin abubuwan da ke haifar mana masifun da muke fuskanta a yandu cikin al’umma.
Hakika wannan wata jarabawa ce da mata suka dorawa kansu, shin kina mace wacce za a kiraki da uwa ta yaya zaki fara aikata wannan mummunar abu haka?
Shin wacce tarbiyya muke tunanin zamu dora yaranmu masu tasowa a kai nan gaba?
Shin mun taba zama munyi tunanin wacce irin kalubalen rayuwa zamu fuskanta ta dalilin wannan aika aikar?
Tabbas duk wacce ta samu kanta cikin irin wannan rayuwa ta hadu da jarabawa matuka.
Haka ana cutar da iyayen yara ta jefa yaransu cikin wannan dabi’a ba tare da saninsu ba bayan sun riga sun basu ingantacciyar tarbiyya daga gida.
wasu yaran kan jefa kansu da kansu ba tare da wani ya tilasta musu ba.
Mu sa ni a duk lokacin da muka kauce fadin Allah dole mu hadu da dana sa ni.
Mu sa ni wannan dabi’a tana iya haifar mana da matsaloli kala kala kama daga ta gangar jiki har zuwa kwakwalwa, me yasa ba zamu bi hanyar da ta dace ba don samun biyan bukatar mu?
Ko yarinya budurwa aka samu da wannan dabi’a bai dace da ita ba kasancewar ta mace da zaa kira ta da uwa watarana, balle macen da ke da igiyar aure a kanta.
Ya salam! Wallahi mata muji tsoron Allah, saboda mune kashin bayan gyara al’umma. Shin bama tuna makomar mu ne?
Wace hujja muke da itada zamu bayar bayan mutuwar mu muna aikata wannan mummunar dabi’a ta madigo?
Wallahi haramcinta mai girmane.
Saboda haka iyaye mata mu kula da mutanen da yaranmu ke muamala dasu ko a gida ko makaranta, mu zama masu matukar sa ido ga yaranmu wajen tafiyar da rayuwarsu na yau da kullum, haka iyaye maza su taimaka wurin ganin tarbiyyar yaransu bata gurbace ba ta dalilin wasu bata gari.
A k’arshe mu sa ni cewar dauwama a cikin wannan dabi’a ta madigo yana haifar da cuta a mahaifa, gaban mace wanda baya jin magani, sannan yana haifar da cutar mantuwa da tabuwar kwakwalwa, yana haifar mutuwar wulakanci ga duk me yinta. Ina kira ga iyaye maza da mata akan kulawa da tarbiyyar yaran da Allah ya basu amanarsu zai kuma tambayesu ranar gobe kiyama.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button