Labarai

Wanda Ya Zagi Annabi (Saw) Ance Yana Fama Da Cutar Damuwa (Depression)

Ismail Sani Isah wanda ya zagi Manzon Allah (SAW) a shafinsa na facebook ance yana da matsala na damuwa wacce ta sanya masa samun tabuwar hankali
Labarin da ‘yan uwa suke sanar dani daga Sokoto, ance yanzu haka yana hannun hukuma, kuma an tafi dashi asibiti domin a tabbatar da lafiyar kwakwalwarsa,datti assalafy ne yayi wannan rubutu.
Ga yanayin yadda siffarsa ta dawo kamar yadda zaku gani a hoto na farko, sakamakon damuwar duniya da ta masa yawa har ya samu tabin hankali kamar yadda akace .

A yanayin bashi da lafiya da damuwa yadda ya koma hoto: Facebook

To amma marar hankali ne zai iya sayen data, ya kunna wayarsa na Android, ya laluba application dinsa na facebook ya hau ya rubuta munanan kalmomi na zagi ga Manzon Allah (SAW)?
Marar hankali zai iya?
A karkashin rubutun da matashin yayi ya zagi Manzon Allah (SAW), ya bayyana cewa ya nemi aiki ne a karamar hukumarsu bai samu ba, to shine don ya huce haushi sai ya zagi Annabi (SAW), ina ruwan Annabi (SAW) da matsalarsa na rashin samun aiki?
Insha Allahu zamu cigaba da bibiyar lamarin muna fitar da sanarwa, har sai gaskiya ta tabbata, kuma anyi adalci
Allah Ka karawa Annabi (SAW) daraja, Ka sanya mu cikin cetonsa Amin.
Karin Bayyani
Ismail Isah shekarunsa 31, yana da zama a unguwar Wangarawa a Sokoto South, amma anfi sanin sunan unguwar da Hilin Boka, gidansu yana ta wajen bayan tsohon gidan marigayi Shagari
Mutanen unguwarsu sun tabbatar mana da cewa Ismail ya taso da karatun addini irin na zaure, sai dai daga bisani ya biyewa son ranshi ya shiga harkan tsubbu ya zama boka, a hakane yaje ya hadu da susucewar kwakwalwa saboda hulda da shaidanun mutane da aljanu
Katin zaben Ismail

Hakanan yake rayuwa cikin kaskanci, yana yawan aikata tabargaza da shirme irin na mahaukata a unguwarsu kafin yanzu da ya tsallaka dandalin facebbok ya zagi Annabin Rahama Muhammad (SAW)
‘Yan uwansa sunyi kokarin boyeshi, to amma munbi wani tsari sai da aka tabbata sun fito dashi aka kamashi, yanzu haka yana kulle a State CID na Sokoto inda za’a gudanar da bincike kafin a gabatar da shi a kotu
Wannan shine hoton zindikin wajen CID Office

Alhamdulillah munyi namu, Allah Ya zama shaida, yanzu hukuma itace tafi sanin dacewa da hukuncin da ya kamata a masa
Allah Ka kara wa Annabi daraja (SAW)Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button