Labarai
An bayar da belin mai shafin Telegram a Faransa
An bayar da belin hamshakin attajirin ɗan asalin ƙasar Rasha kan Dala miliyan biyar da rabi, tare da hana shi barin Faransa.
Mista Durov na fuskantar tuhume-tuhume da dama da suka haɗa da gazawa wajen daƙile ayyukan ƴan ta’adda da abubuwan da ba su dace ba a dandalin musamman yaɗa hotunan cin zarafin yara.
Kusan mutum biliyan ɗaya ne ke amfani da dandalinsa na Telegram.
An dai tsare Mista Durov ne tsawon kwana huɗu a Faransa a wani ɓangare na bincikensa kan aikata manyan laifuka.
Tuni dai lauyansa ya yi watsi da zarge-zargen da ake masa inda ya ce dandalin na Telegram ya kiyaye dokoki da sharuɗɗan amfani da intanet na Turai.
BBC Hausa