Kannywood

A daina ma yan fim kallon yan iska. inji Hauwa Waraka

Advertisment

Fitacciyar jaruma a masana’antar fina-finai ta Kannywood. Hauwa Abubakar, wacce aka fi sani da Hauwa Waraka, ta yi kira ga masu cewa yan fim musamman mata yan iska ne, da su daina yi musu irin wannan kallon, domin kuwa su ma mutane ne, kamar kowa za su iya yin kuskure kuma za su iya yin dai dai, don haka sai a rinka kallon su kamar sauran mutane in dai adalci a ke so a yi musu.jaridar dimokuradiyya na ruwaito.

Hoto :Instagram – Hauwa Waraka

Kowa dai ya san irin rawar da Hauwa Waraka ta ke takawa a cikin yawancin fina-finan da ta ke fitowa, musamman ma wadanda ta yi suna a rol din karuwanci da shirya tuggu, wannan ne ya sa muka yi mata wannan tambayar. In ta ke cewa , “Ba hali na ba ne, yanayin rol din ne haka, kuma idan za a kalle ni a matsayin karuwa ai na fito a fina-finan da dama a wata siffar. Ka ga na fito a matar aure mai hakuri da biyayya ga mijin ta da iyayen ta, don haka fim ne ya ke zuwa da haka” inji ta.
Hoto :Instagram – Hauwa Waraka

Ta ciga ba da cewa, ” Amma yanzu da mu ke magana da kai a natse ka same ni, don haka rayuwar cikin fim daban, wadda mu ke yi a waje daban, domin a fim ana son a nuna fadakar wa ne, yadda mutane za su fahimci sakon, don haka masu kallon mu su gane abin da mu ke yi a fim rayuwar mu ba haka take ba”
A karshe ta ce, “Don haka a daina yi mana kallon ‘yan iska, don babu wanda ya ke so ya ga ya lalace ko wani na sa, don haka idan aka ga mun yi ba dai-dai ba, to a rinka yi mana addu’a ta alheri, ta haka ne za mu gyaru.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

3 Comments

  1. Haba Hauwa Waraka Ai Bahaushe Yana Cewa Halin Mutum Jarinsa. A Masana’antar Kannywood Akwai Wadanda Duk Fitowarsu Basuda Kushe A Cikinta, Dukda Cewa Ana Iya Saka Mutum A Kowane Role, Amma Amfi Saka Mutum A Role Dinda Yafi Iyawa. Akwai Matanda 70% To 80% Role Dinda Suke Yawan Fitowa Na Mutanen Kirki Ne, Amma Gaskiya Ke 85% Na Role Dinda Kike Fitowa Na Mutanen Banza Ne, Kuma Kusan Du Role Dinka Kinfi Fitowa A Karuwa, Kuma Koda A House Wife Kika Fito To A Karshe Neman Maza Zakinayi Ko Kuma Kawo Maza Gidan Mijin Naki.
    Da Zaa Lissafa Fina Finanki Daga Lokacinda Tauraruwarki Ta Fara Haskawa Zuwa Yanzu, Inada Tabbacin Cewa 70% Na Fina Finanki Kin Fitone A Karuwa Ko Mutuniyar Banza, Sabanin Wasu Actress Din Mata. MEYASA?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button