Labarai

Shugaba Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Harin Bom Din Da Aka Kai Wa Jirgin Kasa

Daga Comr Abba Sani Pantami
Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da harin bam da aka kai wa jirgin kasa da ke ɗauke da fasinja kusan 1000 a hanyar Abuja zuwa Kaduna, yana mai bayyana al’amarin a “matsayin wani abin damuwa matuka.”
A cikin sanarwar da fadar shugaban ta fitar, Buhari ya ce, “kamar sauran ‘yan Najeriya, ina cikin jimami matuƙa da faruwar wannan lamarin, wanda shi ne irinsa na biyu, wanda ya kai ga sanadin mutuwar fasinjojin da har yanzu ba a tantance adadinsu ba da kuma wasu da suka samu raunuka.”
“Harin da aka kai kan jirgin kasa, abin takaici ne; tunani na yana kan iyalan waɗanda suka rasu da kuma addu’a ga wadanda suka jikkata,” in ji Buhari.
Shugaban ya ce ya bayar da umarnin gaggawa na tabbatar da bincike da hanyoyin magance matsalar tsaron titin jigin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna.
Sannan ya umarci jami’an tsaro su kuɓutar da fasinjojin da daka sace tare da farautar ƴan bindigar.
Bayanai sun nuna cewa kimanin mutum 1000 ne a cikin jirgin, wanda aka kai wa hari ranar Litinin da daddare.
Rahotanni sun ce an sace mutane da dama sannan an kashe wasu, abin da ya jijjiga iyalai da ‘yan uwan fasinjojin da ke cikin jirgin.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button