Yadda Jarumi Bello Muhd Bello zya musulunta da wata baiwar Allah Ya kuma Aurar da ita


Jarumi Bello Mohd Bello Ya Aurar da Yarinyar data karbi MUSULUNCI ta kuma zabi suna FADIMATU.
Mai nema ya nema wa ‘Danshi (Abdullahi) auren ‘Yar da ALLAH ya bashi, ya kuma baiwa MUSULUNCI (Fadimatu)
Shi kuma ya baiwa mai nema, ya karbawa ‘danshi abisa SUNNAH!
Da wadanda suka taimaka, da masu niyyar taimakawa, duk ALLAH ya sakawa kowa da alkhairi.
A cikin jawabin wani can yayiwa bello Muhammad bello jinjina inda yake mai cewa
“Dan nanayen nan, Bello Muhammad Bello, wanda ya dirtse Abduljabbar akan zagin manzon Allah da yake yi da sahabbansa, ya yi wani aiki da ban taba ji Abduljabbar ya yi ba.
Bayan ta karbi Musulunci, ta zabi suna fadima, ya aura mata wani Abdullahi, kuma zai mata kayan daki!
Abduljabbar sai dai ya sa wa wasu shubuha su iya barin addinin ma!”
Wanda a cikin wannan bidiyo zaku ga yadda alamarin ya faru.


