Kannywood

Tsakani na da Afakallah da Momee Gombe – Sunusi Oscar

Darakta Sunusi Oscar 442

SUNUSI Hafiz, wanda aka fi sani da Sunusi Oscar442, ya bayyana abin da ya tsaya masa a rai, wanda a kullum da shi ya ke kwana ya ke tashi, kuma shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah), shi ne ya aikata masa abin. Shin wane abu ne wannan? Bayan haka, ana yawan ganin jaruma Momi Gombe tare da fitaccen daraktan, har ta kai ga babu jarumar da ya ke sanyawa a aikin sa kamar ta. Shin menene dalilin?
Wani abu game da Sunusi Oscar shi ne ya yi fice wajen bada umarni a gun shirya finafinai, to amma a ‘yan shekarun nan sai ya juya akala zuwa bada umarni a waƙoƙin da ake ɗauka ana sakawa a YouTube. Me ya janyo hakan?
A cikin wata tattaunawa ta musamman da ya yi da mujallar Fim, daraktan ya bayyana dalilan waɗannan al’amurra. Ga yadda hirar ta gudana:
FIM: Mai karatu zai so ka gabatar masa da kan ka.
SUNUSI OSCAR442: Suna na Sunusi Hafiz, wanda aka fi sani da Sunusi Oscar, da ke zaune a Jihar Kano, a kuma masana’antar Kannywood ta Jihar Kano. Kuma Oscar wani mutum ne kawai da ke shirya fim a Jihar Kano. Sannan ba kowa ba ne ba, wanda a yanzu haka mun kai kusan shekara talatin ana gwagwarmaya a wannan masana’anta.
FIM: Me ya sa yanzu ka fi karkata wajen wasu ƙananan jarumai fiye da manya?
SUNUSI OSCAR442: Shi fim ya na buƙatar lokaci. To duk mutumin da zai ɗauki lokaci ya ba ka za ka ji daɗin aiki da shi, duk wanda ba shi da lokaci a kan abin da za ka yi to ba zai bar ka ka yi abin da ka ke so ba, ko waye shi kuma duk iyawar sa. Duk girman sa a masana’antar to zai ɓata maka abu ne saboda ita masana’antar an gina ta ne a kan bin wasu mutane daban, ba wai yin wani abu na gaskiya ba. Shi ya sa mu ke shan wahala, mu daraktoci, domin mu na ta bibiya, mu bi wannan jarumi mu bi wannan jaruma, don mu na son fim ɗin mu ya samu ɗaukaka, wanda kuma ba wai shi ba ne ba.
A matsayi na na darakta, ni na ke da abin cewa a kan abu na ya yi kyau ko da wane irin mutum na ɗauko, mace ko namiji, baƙo ko baƙuwa. Ba na buƙatar wani jarumi dattijo wanda zai zo ya ɓata min lokaci, ya zo ya yi min iya yi, ga tsada ga iya yi, daga ƙarshe ma aikin naka ya zo ya ɓaci, fim ɗin ka ya lalace, mutanen gari su dinga tunanin ba ka da labari mai kyau. Kuma matsalar ba daga kai ba ne, matsalar daga su jaruman da ka tara ne, don ka na son fim ɗin ka ya ɗaukaka, amma sai su ƙi ba ka cikakken lokacin da ya kamata don aikin ka ya yi kyau. Shi ya sa ba ruwa na da wani maganar ɗaukakakken jarumi! Na kan yi fim da duk wanda na ga dama, duk wanda labari na ya kirawo shi zai bai wa labarin abin da ake so, ya ban lokaci za mu yi aiki da shi, mu yi lafiya mu gama lafiya, mu kai kasuwa kuma mutane su yaba.
FIM: Kenan babu ruwan ka da ɗaukakar jarumi ko rashin ɗaukakar sa?
SUNUSI OSCAR442: To ai ita ɗaukakar jarumi, a nan masana’antar fim ne ma jaruman mu su ke da wannan ɗaukakar, amma shi darakta shi ne gaba da komai. Jarumi ba shi da wani ikon da zai nuna maka cewa shi isasshe ne, kuma ban ga dalili ba; idan ya yi maka abin da ba daidai ba a lokeshin, ya kamata ka kore shi, ka cire shi; ko kuma idan ya saɓa dokar da ku ka yi da shi ka maka shi a kotu kawai, ba shi da wani amfani a gurin ka. Duk mutumin da ba zai ɗauki sana’ar da ku ke yi da muhimmanci ba, rayuwa da shi ina ganin ba dole ba ne.
FIM: Wace irin yarjejeniya ku ke yi da jarumi wadda idan har ya karya ta za ta kai ku ga zuwa gaban alƙali?
SUNUSI OSCAR442: Ka na da yarjejeniya za ka ba wa mutum fom ya cike, ya sa maka hannu, ya yarda da kaza, za mu fita fim kaza, za mu gama shi zuwa lokaci kaza; kai ma kar ka saɓa masa wannan dokar. Don haka duk wanda ya saɓa maka wannan dokar ka na da hujjar da za ka ɗauki doka a kan shi, ko waye shi.
FIM: Ana cewa kai ne daraktan da ya fi kowa rainon jarumi ya samu ɗaukaka a Kannywood, amma daga baya sai su juya maka baya ko su koma wajen wani, su bar ka. Shin ya ka ke ji da irin wannan halin na wasu jaruman?
SUNUSI OSCAR442: Gaskiya ne wannan, saboda ita kan ta masana’antar ta na buƙatar matasan jarumai maza da mata, don haka lokacin da na raina domin ni abin da na ke yi kenan, in raina, ita kuma masana’antar sai ta kai caffa a kan su domin ta ci gaba da aiki da su, domin ita ta kasa rainon yaran don haka dole abin da na raina da shi za ta yi aiki. Ba wai ƙwacewa ake ba ko makamantan su; in ma yaro ya tafi, ya san ni uban sa ne. Ko da an canza masa tunani a kan wani abu, ba zai manta baya ba, kuma ‘yan kallo za su tuna cewar “a lokacin da na ga jarumi wane ko jaruma wance, daga hannun wane na fara ganin shi”.
Don haka ni abin ba ya damu na ko kaɗan. Daga ran da na ɗauko jarumi ko jaruma, ji na ke a wannan lokacin tamkar mun rabu ne ma, ba na sa shi a rai na wai za mu dauwama da shi. Ban taɓa sawa a rai na ba ko wace irin jaruma ko jarumi ban taɓa sawa a rai na ba. Kawai dai na ɗauko ka, na san cewa idan na koya maka in ka samu cigaban abin da na ke fiye da nawa, to ka yi gaba. Ba laifi ba ne ni a guri na.
FIM: A tsarin masana’antar, kafin a fara ɗaukar fim sai an ba jarumi labari ya duba kafin ya fito a fim. Shin ko ka taɓa samun wata magana mara daɗi daga bakin wani jarumi kan labarin ka kafin ya amince?
Shugaban hukumar tace fina finai Ismail Na abba Afakallah

SUNUSI OSCAR442: A gaskiya jaruman da mu ke mu’amala da su su na girmama aikin da mu ke tare da su, domin kuwa ba na mantawa akwai wani fim ɗi na na kai na da zan yi, akwai jaruman da su ka karanta labarukan wajen sau uku zuwa huɗu, da kan su su ka gaya min cewar mu fito mu yi fim ɗin nan, “kai ga ma gudunmawar mu a cikin yin fim ɗin” domin jin daɗin yadda ake aikin da jin daɗin labarin. Kuma sun san abu mai kyau za a yi. Don haka ni ba ni da wani ƙalubale a kan wannan abin a rayuwa.
FIM: A baya bayan nan ana ganin cewa ka fiye sa Momi Gombe a cikin waƙoƙin da ka ke yi. Yaya alaƙar ka ta ke da ita?
SUNUSI OSCAR442: ‘Ya ce a guri na. Ta ɗauke ni tamkar mahaifin ta, don haka na ke mata zamantakewa irin wannan. A duk lokacin da mutum ya kawo aiki, na kan tuntuɓe shi ya na da wanda zai sa? Idan ya ce babu, sai na ce, “To ina so ka taimaka na saka wance.” Shi ya sa mutane su ke ganin ayyukan ta da yawa. Ba wani abu ba ne ba. Kuma ba ta nisa da ni; duk inda na ke a Nijeriya, in dai na fita ɗaukar fim, ko ba da ita zan yi ba, za ta ce min, “Daddy ka na ina? To ni ma zan zo.” To wani lokacin idan ta zo sai a yi katari idan mu na da buƙatar wani abu sai kuma ta zo ka ga ta yi abin. Wannan shi ne mafi yawan nasarar da ta samu a rayuwar ta.
Wani abu kuma a kan jarumar, akwai yarda da jagoranci, kuma ba ta da irin zuciyar sauran wasu daga cikin yaran na butulci. Ta na da ƙoƙarin daurewa; ko da zamantakewar da ake babu daɗi, amma ta na daurewa da zamantakewar da ake yi. Na yaba mata sosai a kan haka, ba ɗaya ba ba biyu ba, a kan wannan abin da ta yi a rayuwar ta.
FIM: Da man ka san ta ne a baya?
Momee Gombe, ‘yar gidan Oscar. “‘Ya ce a guri na. Ta ɗauke ni tamkar mahaifin ta,” inji Sunusi Oscar.

SUNUSI OSCAR442: A’a, ban san ta ba. Wannan harkar ce ta haɗa mu da ita kuma mu ka zauna mu ka yi magana da ita, ga yadda na ke so mu zauna tare a ƙarƙashi na, na ɗora mata dokoki, ta yarda, ta gamsu. Kai, kawowa yau ban ga saɓanin abin da mu ka yi da ita ba.
FIM: Bayan ita, ko akwai wasu waɗanda ku ke shirin raino nan gaba?
SUNUSI OSCAR442: Akwai su. Yanzu na taso da mutum huɗu, kuma in-sha Allahu mu na sa ran nan ba da daɗewa ba duniya za ta gamsu domin mun fara aiki tare da su. A yanayin da na yi musu kallo, irin waɗanda za su yi saurin karɓuwa a wurin al’umma ne.
FIM: To wane dalili ya sa ka ɗauke ƙafa daga harkar shirya fim, ka koma waƙoƙi kacokam?
SUNUSI OSCAR442: To, ina da matsala da shugaban Hukumar Tace Finafinai. Ba ya ƙauna ta gaba ɗaya, don haka ba wani abu da zan iya yi don in rayu a masana’antar Kannywood in dai ya na nan. Sau da yawa zan yi fim, zai ce in dai ni ne ba zai duba fim ɗin ba. A satin nan ma akwai wani fim ɗi na da na yi, na kamfanin Sheshe, ya ce a cire suna na, in dai ni ne fim ɗin ba zai fita a cikin Jihar Kano ba. To mai kamfanin ya sa aka kira ni, ya ce ga abin da Hukumar Tace Finafinai ta gaya masa. Na ce masa ya yi haƙuri a cire, ba wani abu ba ne ba. Haka aka cire, aka maye suna na da na Ali Gumzak a cikin wannan fim ɗin. Don haka wannan ba na jin za a min adalci.
Ban san me na yi masa ba ya ɗaure ni. Don haka ga finafinai na da yawa a ƙasa, kusan aƙalla ina da fim na wajen miliyan 7 ko 8, yanzu haka sun zame min asara domin idan na kai ba zai bari a duba ba, sai dai na ajiye abu na a kwalla. Ka ga shi ya sa na koma waƙa. Waƙa ba ta da maganar kasuwanci na Jihar Kano, don ba sidi ma yanzu, ba dibidi, in ma kawai yanzu za mu sa a yanar gizo ko YouTube da yawa kuma mutane ta nan su ke kallo. Kuma mu na ci gaba da aikin, ba mu fasa ba. Amma fim mu na nan a cikin shi, kuma za mu dawo tunda shi ma ba zai dauwama ba. In mu na raye ni da shi, kuma ba mu mutu ba, to zan dawo Jihar Kano zan ci gaba da fim, shi kuma a lokacin ba ya hukumar.
Darakta sanusi oscar 442 kwankwasiyya Amana

FIM: Ya alaƙar ka ta ke da sauran takwarorin ka daraktoci?
SUNUSI OSCAR442:  Ni ban da wata matsala da wani darakta a masana’antar nan gaba ɗaya. Ina da kyakkyawar alaƙa ni da su, mu na zama wuri ɗaya mu yi hira. In ma ban gan su ba ko ba su gan ni ba, su na tambaya ta ko su tuntuɓe ni su tambaye ni ina ina? “Ina ka shiga kwana biyu?” Na ce musu ina nan ƙalau. Haka mu ke zaune tare da su. Ni ba mu taɓa samun matsala da wani darakta ba.
FIM: A tsawon iya shekarun da ka yi a wannan masana’anta, wane abu ne ba za ka taɓa mantawa da shi ba a rayuwar ka?
SUNUSI OSCAR442: Ka san wani lokacin tuna irin abubuwan da su ka wuce ma ba shi da wani amfani, amma zai yi wahala a manta da abin da ya ke mafi sharri ko mafi alkairin cikin sa. Ba abin da ya ke damu na a zuciya ta, kuma na ke kwana da shi na ke tashi da shi, irin yadda shugaban Hukumar Tace Finafinai ya ɗaure ni. Shi ne wannan abin da ya fi damu na a rayuwar duniya, domin ni na san cewar ban aikata komai ba, wani abu ne nashi na karan kan sa, don son zuciyar sa, ya yi. Amma ni na san cewar akwai lokaci; in ma ya yi ne da wata manufa, Allah ya ba mu rai da lafiya!
FIM: Wane kira za ka yi daga ƙarshe?
SUNUSI OSCAR442: To kira na shi ne wannan hukuma ta tace finafinai ta yi ƙoƙari ta san cewa akwai Allah, ta yi mana adalci mu ‘yan PDP da mu ke yin PDP Kwankwasiyya. Su daure su yi mana adalci, su ɗauke mu ba maganar jam’iyya, su ɗauke mu a matsayin masu kasuwancin fim, su yi mana adalci, kar su hangi wani soyayya tsakanin mu da Kwankwaso domin duka wanda ya ke yin Ganduje a cikin Jihar Kano, ɗan fim, mu na zaune da shi lafiya, ba ma faɗa da kowa. Haka ni ma bai kamata hukumar ta dinga faɗa da ni ba don ina yin wani ra’ayi ba, don wannan shi ne matsala ta da shi (Afakallah), don ban da matsala da shi bayan wannan. Yau da zan koma jam’iyyar APC, to da ni da shi za ka ga mu na yawo tare. Kawai dai bambancin siyasa ne, amma ba abin da na yi masa. Shi ma kuma ya sani. Ya ɗauko Ƙur’ani izu sittin ya dafa ya ce akwai wani abu bayan wannan, ka ga in bai ci shi ba!
Mun dauko wannan tattaunawa daga shafin fimmagazineMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button