Labarai

An kama Ɗan da Uba Masu Safafar Bidigogi Ak-47 suna Kaiwa Yan Ta’adda A katsina

Advertisment

‘Yan sandan jihar Katsina sun kama wasu mutum 4 da suka tsere da bindiga kirar AK-47 suke kaiwa ‘yan ta’adda..
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce tayi nasarar cafke wasu mutum 4 da ke kaiwa ‘yan fashin daji bindigogi kirar AK-47 a jihar Katsina ciki har da dan shugaban kungiyar mai sunan Ibrahim Abdullahi dan shekaru 40 da haihuwa. Kuma sun gano wasu kudi naira Miliyan 3 da dubu dari hudu (N3.4m) a hannun su.

Kudin da anka samu a wajen masu safarar makamai kenan

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, Sufeto Gambo Isah, wanda yayi holar masu laifin a gaban ‘yan jaridu tare da wasu mutum 7, yace an gano wadancan kudade ne a cikin Babura biyu.
Gambo Isah, ya kara da cewa wasu jami’an tsaron ‘yan sanda masu sintiri akan tsitin Tsaskiya Ummadu a karamar hukumar Safana jihar Katsina su ne suka kamo masu laifin.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button