Kannywood

An hana wakokin yabon Annabi a Kano sai da izinin gwamnati

Hukumar tace fina-fanai da sauran adabi ta jihar Kano ta ce babu wani sha’iri da zai kara waka a jihar sai idan ta ba shi lasisi.

Shugaban hukumar Isma’il Muhammad Na’abba wanda aka fi sani da Afakallah ne ya bayyana hakan a wata hira da BBC ta yi da shi.
Afakallah ya ce ganin yadda sha’irai ke wuce iyaka a lokuta da dama ya sa hukumar ta dauki wannan azama.
Ya kuma ce ko an bai wa sha’iri lasisi idan ya yi wakar sai ya kawo an saurara an tabbatar da babu wani abu na batanci a ciki.
Isma’il Muhammad Na’abba ya ce an kafa wannan hukuma ne kan abu uku kan harkokin addini cikin abubuwan adadi, da al’adu da kuma zamantakewa ta yadda kowa zai girmama addini da al’adar abokin zamansa.

Wannan layi ne

Ya zuwa yanzu in ji Afakallah ya ce akwai wakoki uku zuwa biyar da suka taba rikita jihar Kano sakamakon rashin tantancewa.
“A baya mun ba su damar tace wakokin da suke yi ta hanyar jagorancin wasu shugabanninsu amma sai abin ya zo da rikici shi ya sa a yanzu muka dawo da ragamar aikin hannunmu.
”Abin yana ci mana tuwo a kwarya ganin ganin yadda ake shiga hurumin Allah da Annabinsa, da kuma yadda ake zagin manyan bayin Allah duk da sunan yabo,” in ji Afakallah.
Shugaban ya ce mutanen jihar Kano masu riko da addini ne don haka suka fara yunkurin daukar mataki da kansu a baya kan irin wadannan abubuwa, don haka gwamnati ta farga kuma da sannu za a yi wa tufkar hanci.

YoutubeHakkin mallakar hotoYOUTUBE
Image captionZa a rika bai wa irin wadannan mawaka horo domin sanin me suke wakewa da kuma kalaman da ya kamata su rika amfani da su

Afakallahu ya ce “Tuni muka nemi gidajen rediyo a Kano su daina sanya irin wadannan wakoki har sai lokacin da muka bayar da izini”.
Da aka tambaye shi ganin cewa ba su da adadin mawakan da ke jihar sai ya ce: “A ko wacce karamar hukuma muna da ofishi kuma ko wanne ofishi da kayan aikin da za a iya aikin tace waka a cikinsa don haka ba abu ba ne da zai ba mu wuya wajen shawo kansa.
Mun tanadi hukunce-hukunce da za mu yi wa duk wanda ya karya dokar da aka shimfida, domin mu tabbatar da ya zama izina ga ‘yan baya.”
Za a rika bai wa irin wadannan mawaka horo domin sanin me suke wakewa da kuma kalaman da ya kamata su rika amfani da su.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button