Mutum 13 sun rasu a hatsarin jirgin ruwa a Sokoto
Mutum 13 ne suka rasu dukansu mata da kanana yara a cikin wani hadarin jirgin ruwa a jihar Sakkwato da ke shiyyar arewa maso yammacin Najeriya.
Lamarin dai ya faru ne da yammacin jiya Alhamis a yankin karamar hukumar Shagari da ke kudancin jihar kamar yadda kamfanin dalancin labarai Bbchausa na ruwaito.
Hadarin dai ya faru ne mako daya daidai bayan da wani hadarin jirgin ruwa ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 100 a makwabciyar jihar Kebbi.
Kamar lamarin da ya faru makon jiya daura da garin Warah na jihar Kabbi, kwale-kwalen ya kife ne lokacin da matafiyan ke da daf da kai wa inda za su domin hidimar aure.
Jirgin dai ya taso ne daga garin Ginga dauke mutum 18, amma sai ya kife daf da ƙauye Doruwa inda ya nufa; lamarin ya yi sanadin mutuwar mutum 13 yayin da biyar suka tsira.
Alhajo Aliyu Dantine Shagari shi ne shugaban karamar hukumar Shagari inda lamarin ya faru kuma ya ce tuni da suka yi jana’izar wadanda suka rasu.
Yayin wata ta’aziyya da ya kai a garin Ginga inda mamatan suka fito a dazu, gwamnan jihar ta Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya yi samar wa al’umomin yankin da jiragen ruwa masu injin da kuma rigunan hana nutsewa a ruwa don kare afkuwar hakan a gaba.
Ko a watan Agustan bara ma mutane tara sun rasa rayukansu a cikin hadarin jirgin ruwa makamancin wannan a yankin karamar hukumar Goronyo da ke gabashin jihar ta Sakkwato.