Labarai

Subhanallahi ! Kashe-Kashen Arewa: Zan Maka Buhari da Manyan Sojoji Zuwa Kotun Hukunta Ta’addanci na Duniya — Dakta Idris Ahmed

Daga Yahaya Muhammad Soje

Daya daga cikin Yan Kasar Nijeriya Mazauna Birnin Coventry a Kasar Burtaniya Dakta Idris Ahmed, ya dau ma kansa alwashin rubuta takardan koke a kan shugaban Kasar Nijeriya Buhari da manyan hafshin sojojinsa zuwa kotun hukunta manyan laifuka da ta’addanci na duniya dake birnin Hague a Kasar Netherland, bisa tuhumar shugaba Buhari da laifukan yaki da laifukan take hakkin bil’adama, kamar yanda ake gudanarwa yanzu a Arewacin Nijeriya.

Kwanakin baya Idris Ahmed ya kasance babban jigo wanda yayi gwagwarmaya da ilminsa da dukiyarsa wajen tabbatar da nasaran shugaba Buhari tun daga wa’adin mulkinsa na farko da na biyu don ganin Buhari ya samu Nasara, Inda ya bayyana wannan Jaricewar a matsayin Kuskure.

Sai dai sakamakon yadda lamura suka canza a kwanakinnan musamman a kan yanayin tsaron Nigeria, Dr Idris ya dawo daga rakiyar shugaban Kasa Buhari inda ya fara kalubalantarsa musamman kan abubuwan dake faruwa yanzu haka a yankin Arewacin Nijeriya.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button