Miyagu Za Su fara Amfani Da NIN Don cutar ‘yan Najeriya – NIMC
Hukumar samar da katin ɗan ƙasa a Najeriya ta National Identity Database in Nigeria (NIMC) ta gargaɗi jama’a da su kiyaye da sabbin saƙonnin da wasu miyagu za su fara turo musu suna masu iƙirarin cewa su ma’aikatan MTN ne ko Airtel ko 9Mobile ko Glo.
Cikin wata sanarwa da ta wallafa, NIMC ta ce: “Cikin ‘yan kwanaki masu zuwa masu zamba za su fara turo muku saƙon cewa an tura muku wani rukunin lambobi na neman tantance lambar shaidar ɗan ƙasa ta NIN, saboda haka ku sake aiko mana da ita.”
NIMC ta ce sake aika musu da lambar ka iya jefa mutum cikin haɗarin cuta, ta yadda za a iya amfani da bayanansa wurin sabunta layin da ya ɓata da kuma yin sayayya da sunansa ta intanet ba tare da ya sani ba.
“Ba za su tambaye ku lambobin BVN ba ko NIN ko bayanan katinku, saboda za a gano su da wuri. Muna roƙonku da ku share irin wannnan saƙonnin kawai.
“Idan kamfanin layin da kuke amfani da shi ya kasa tantance lambar NIN ɗinku, za su nemi ku je ofishinsu ne domin yin hakan.”
Bbchausa nayi kokarin tattara wannan bayyani a makon da ya gabata ne hukumar sadarwa ta Najeriya NCC ta bayar da umarnin rufe duk wani layin waya da ba a yi masa rajista da lambar ɗan ƙasa ba ta NIN cikin mako biyu.
‘Yan Majalisar Tarayyar Najeriya sun yi umarni da a ƙara wa’adin zuwa mako takwas amma hukumar ta ƙeƙashe ƙasa ta ce umarninta mako biyu na nan daram.
Beware of Fraudsters, be #CyberSmart.#DigitalNigeria @DrIsaPantami @NgComCommission @FMoCDENigeria pic.twitter.com/N8F5Oe2UB7
— NIMC (@nimc_ng) December 19, 2020
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)






