Labarai

Gwamna Tambuwal Ya Shedi Daurin Auren Abdullahi Shehu Dan Kwallon Nigeria A Kano ( Hotuna)

Advertisment

Maigirma Mataimakin Gwamnan Jihar Sokoto Hon. Muhammad Manir Dan Iya (Walin Sokoto) ya wakilci Maigirma Gwamna jihar Sokoto Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal CFR (Mutawallen Sokoto) a wajen Daurin Auren Shahararren Dan Wasan Kwallon kafa ta duniya waton Super Eagle Abdullahi Shehu dake Sokoto a garin Kano.
An daura auren Abdullahi Shehu ne da Amaryar sa Naja’atu Muhammad a masallacin Umar Bin Alkhadtab dake garin Kano bayan an biya sadaki Naira dubu 50.
Maigirma Jarman Sokoto Amb. Alh Dr Ummarun Kwabo A.A MFR (Uban Marayu) na daga cikin mahalarta daurin auren tare da mukarraban sa.
Mataimakin Gwamnan na tare da Rakkiyar Kwamishinan matasa da wasanni na jihar Sokoto Comr Bashir Gorau da sauran su.
Jama’a da dama daga Sokoto sun halarci Daurin Auren, kama daga Tawagar ‘Ya’yan gidan Gwamna Tambuwal, ‘yan uwa da abukkan arziki, haka ma babban abokin sa Shahararren Dan wasan kwallon kafa na super Eagle Ahmed Musa daga jihar Kano na daga cikin mahalarta daurin auren.
Allah SWT bada zama lafiya da zuri’a dayyaba, ya kuma mayar da Tawagar jihar Sokoto da Abuja gida lafiya don darajar Alkur’ani Maigirma
Bilya Yariman Barebarin Fcbk
Jumu’a 18th June 2021.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button