Labarai
Shugaba Buhari ya Kori Ministocin shi biyu
Advertisment
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya Kori Ministan Noma Mohammed Sabo Nanono, da kuma takwaran shi Mamman Saleh na fannin wutar Lantarki.

Mai magana da yawun Fadar Shugaban kasa Femi Adesina ne ya bayyana hakan, ya yin da yake zantawa da mane ma labarai a yau Laraba a garin Abuja babban birnin Nigeria.

Kazalika nan take ya bayyana cewa, dukkannin wadanda aka Koran, an maye gurbin su da Ministan Muhalli Mohammed Mahmoud Abubakar da kuma karamin Ministan aiyuka da gidaje Abubakar Aliyu. Wanda sanarwar Koran na su ya fara aiki nan take.



