Labarai

Yadda Aka Hallaka Ahmad Gulak Da Bidiyon Gawarsa (bidiyo)

Dazu da safiyar yau Lahadi 30-5-2021 da misalin karfe 7:20am na safe ‘yan ta’addan IPOB suka tare motar da Ahmad Gulak yake ciki kirar Toyota Camry yana tare da mutane biyu akan hanyarsa na zuwa filin jirgi na Sam Mbakwe Airport inda zai hau jirgin da zai kaishi Abuja, ‘yan ta’addan sun cireshi a cikin motar suka harbeshi har lahira
Rundinar ‘yan sandan jihar Imo tace Ahmad Gulak ya bar hotel dinsa zuwa filin jirgi ba tare da ya sanar da wata hukuma na tsaro ba, lura da yanayi na rashin zaman lafiya a yankin, shiyasa bai samu kariya daga hukumomin tsaro ba, direban da yake jansa a mota sai yabi hanyar da take da hatsari wanda hakan ya kai ga an tare motar aka kashe shi
Datti Assalafy ya fitar da wannan  bayyani ‘Yanta’addan na IPOB sun zo ne a cikin mota kirar Toyota Sienna su 6, kuma Ahmad Gulak kadai suka kashe a motar suka gudu, yanzu dai ‘yan sandan jihar Imo sun bazama a yankin domin gano wadanda suka aikata ta’addancin


 
Mutane biyu da suke tare da marigayin ba’a kashe su ba, sun gudu sun bar motar, kisa ne mai kama da hadin baki
Muna cikin wani irin yanayi da rayuwar ‘yan Arewa a jihohin Inyamurai take cikin hatsari, kawai da zaran sun ganka da siffa irin na ‘yan Arewa sunanka matacce, yayin da su kuma mutanensu gasu nan a garuruwan Arewa suna zaune kalau cikin aminci
Ya kamata Gwamnatin Nigeria ta ayyana cikakken yaki da IPOB, masu goyon bayansu a batar da su, muna son zaman lafiyar Nigeria fiye da komai
Allah Ka jikan Ahmad Gulak, Ka yafe masa laifukansa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button