Labarai
Sojoji Civilan JTF sun Kubutar Manoma shinkafa Sama 200 Daga Boko Haram (Hotuna)
Rahotanni dake shigowa yanzu na cewa sojojin kundunbala da mayakan Civilian JTF sun kubutar da mutanen kauyen Zabarmari manoman shinkafa a kalla 200 daga ‘yan ta’addan Boko Haram
Majiyarmu ta samu daga shafin Voa Idan ba’a manta ba, ranar lahadi da ta gabata ne ‘yan ta’addan Boko Haram suka yiwa mutanen Zabarmari 43 kisan gilla ta hanyar yankan rago, sannan suka tafi da daruruwan mutane jeji
Jinjina gareku sojojin Nigeria, hakika sunyi abin a yaba musu bisa kubutar da mutanen da sukayi daga harin karnukan wutar jahannama tsinannu ‘yan Boko Haram
Allah Ka taimaki sojojin Nigeria akan Boko Haram Amin.