An gano cewa, Mutuminnan farar fata da aka kama me baiwa ‘yan Bindiga horo, Tsohon Sojan kasar Faransa ne
Mutuminnan da kwanaki labarinsa ya karade kafafe da yawa wanda aka kama a kasar Africa ta tsakiya, CAR, tsohon Sojan Faransa ne.
An kuma Gabo cewa, Tun a shekarar 2013 ya ke baiwa ‘yan Bindigar kasar,CAR horon yaki, a yanzu dai a karin farko an Gurfanar dashi gaban Kotu.kamar Yadda Hutudole na ruwaito.
Wasu na tunanin kasar Faransa ba zatavrasa Masaniya da wannan mutumin ba, dalili kuwa shine, kasar CAR ta kawar da akalarta daga kasar faransa zuwa Rasha wajan neman taimako kan harkar tsaro.
Wannan dalili yasa wasu ke tunanin Faransar ta aiko irin wancan mutumin dan ya gurgunta alakar kasar CAR da Rasha.
Faransa na kara samun tawaya a dangantakarta da kasashen Nahiyar Africa.
The French man that was caught in the Central African Republic with large caches of arms and money was a former French soldier. Do you really think he was acting without the knowledge of the French government? pic.twitter.com/h3yU2rCoez
— Defense News Nigeria (@DefenseNigeria) June 11, 2021