Labarai

An Fasa Aure Bayan Amarya Ta Gano Angonta Na Da Sanko

An tashi baran-baran a wani biki da aka yi a Indiya bayan amaryar ta ki yarda a daura aurenta da angonta ana tsaka da shagalin bikinsu, saboda ta gano yana da sanko.
Shirye-shiryen aure abu ne da ya zama ruwan dare a Indiya, amma duk da iyalan ma’auratan sun jima suna tsarawa da tattaunawa a kan bikin, amma duk da haka sai da aka samu matsala.
Wani lokaci daga bangaren amarya. Wani lokacin akan samu tangarda sakamakon rashin sanin wanda za a aura.jaridar Aminiya trust na ruwaito
Misali, wani daurin aure da aka yi kwanan nan a Gundumar Etawah da ke birnin Kanpur a Jihar Uttar Pradesh, inda amaryar ta ki amincewa da a daura aure bayan ta gano cewa angonta yana da sanko.
A cewar jaridar Times of India, komai yana tafiya yadda aka tsara ne, inda an riga an yi musayar furanni tsakanin ma’auratan, amma sai aka samu tangarda a lokacin da amaryar ta lura cewa mijin da za ta aura ya sanya kayan gargajiya da yawa a kansa don boye sankonsa.
Nan take ta fada wa wani a cikin ’yan tawagarta don bincika ko a zahiri yana da sanko ko kuma yana sanye da sumar bogi ne.
An bayyana cewa matar ta kadu da wannan fallasa, sai ta tunkari angon a kan lamarin, inda bayan ta tabbatar da cewa ba shi da suma sai sanko, sai
ta sume nan take.
Lokacin da ta dawo hayyacinta, amaryar ta ki zama a ci gaba da yin bikin auren, inda ta sanar da danginta cewa, ba za ta auri mai sanko ba a kowane hali.
’Yan uwan matar sun yi kokarin gano wani dalilin matar ba ya ga na sanko amma babu, inda suka rarrashe ta, don haka ba su da wani zabi, illa su gaya wa dangin ango cewa an fasa yin daurin auren.
Hakan bai yi wa ’yan uwan mijin dadi ba, kuma an yi ta ce-ce-ku-ce, wanda a karshe dangin amarya suka zargi dangin ango da yaudarar su ta hanyar rashin bayyana halin da gashin nasa ke ciki.
A karshe, dattawan kauyen sun shiga tsakanin ma’auratan ta hanyar kwantar da hankulansu, daga bisani iyalan ma’auratan biyu suka watse.
Sai dai a cewar rahoton ’yan sandan yankin, bangarorin biyu sun kammala gabatar da korafin junansu, inda bangaren dangin amaryar suke ikirarin an yaudare su.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan yankin ya ce, “Daga baya ma’auratan biyu sun janye kokensu tare da warware matsalar a tsakaninsu.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button