Labarai

‘Yar Shekaru 21 Ta Kashe Biloniya Mai Shekaru 50 A Gidan Shi (hotuna da bidiyo)

Chidimma mai shekaru 21 wacce daliba ce a Jami’ar Lagos ta kashe saurayinta mai shekaru 50 wanda shine Shugaban Kamfani Super TV da ke Lagos.

Chidimma

Chidimma ta ce ta tafi gidan shi in da suka kare shaye-shaye kuma ta gaji tana jin barci amma ya ki barinta ta yi barci daganan sai gardama ya kaure a tsakaninsu inda ta dauki wuka ta rinka daba masa har ya mutu sannan ta sulale abinda zuwa gidansu.
Majiyar Zuma Times Hausa ta Punch ta bayyana cewa bayan haka nan Chidimma ta dauki katin ATM dinsa inda ta je ta dinbi darurrukan kudi duk da bincike ya nuna tana da wajen miliyon 10 a asusunta na banki.
Chidimma

Shi dai wannan biloniya yana da matarsa da yaransa wadanda suke zaune a Abuja inda aka ce matar ta shirya masa bikin zagayowar cika shekaru 50 da haihuwa tana jiran zuwansa.
Ga bidiyo nan da shafin lindaikeja na wallafa a shafinta na sada zumunta yadda manema labarai ke yi mata tambayoyi.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

  1. Pingback: Har yanzu ana ya yi na a masana’antar Kannywood - Fati Bararoji – HausaLoaded.Com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button