Labarai

Dan Najeriya ya yi wuff da tsaleliyar matarsa ‘yar Amurka bayan ta yi masa tayin soyyar ta

Wani dan Najeriya ya bayyana yadda rayuwar su ta kasance da baturiyar matar sa
Kamar yadda ya ce, baturiyar da kan ta ta yi ma sa tayin soyayyar ta ta Facebook
Ya wallafa hotunan su tare da zankadediyar matar ta sa cike da shaukin soyayya
Wani dan Najeriya ya wallafa yadda rayuwar sa da zukekiyar matarsa ‘yar Amuka ta kasance bayan ya aure ta kamar yadda LIB ta ruwaito.
Kamar yadda ya wallafa hotunan su har da hirar su ta farko da su ka yi a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, wanda ya yi wa take da ‘Yadda aka fara da yadda ake ci gaba da rayuwa’.
Dan Najeriya ya yi wuff da tsaleliyar matarsa 'yar Amurka bayan ta yi masa tayin soyyar ta Dan Najeriya ya yi wuff da tsaleliyar matarsa 'yar Amurka bayan ta yi masa tayin soyyar ta Dan Najeriya ya yi wuff da tsaleliyar matarsa 'yar Amurka bayan ta yi masa tayin soyyar ta
Cike da soyayya, ya wallafa wasu zafafan hotunan da su ka dauka tare, kuma alamu su na nuna su na matukar kaunar juna.
Da farko ya fara wallafa hotunan hirar sa da matar inda ya nuna yadda ta fara tura ma sa hoton ‘yan aljanun nan na hirar kafafen sada zumunta ma su dauke da alamar soyayya
Baturiyar ta yaba da kyawun sa.
Ta fara da ce ma sa kyakkyawa kuma ta bukaci sanin idan shi dan nahiyar Afirka ne.
Ya sanar da ita cewa shi cikakken dan Najeriya ne daga nan ta ke sanar da shi ita baturiya ce ‘yar Amurka.Dan Najeriya ya yi wuff da tsaleliyar matarsa 'yar Amurka bayan ta yi masa tayin soyyar ta
Ta nuna ma sa farin cikin ta kwarai da ta samu damar zantawa da shi cikin ladabi.
Matashin ya nuna yadda cike da girmamawa da mutumtaka baturiyar ta gabatar ma sa da ra’ayin ta na soyayya da shi.Dan Najeriya ya yi wuff da tsaleliyar matarsa 'yar Amurka bayan ta yi masa tayin soyyar ta
Daga wallafar ta sa za ka gane yadda yake madalla da auren baturiyar.
Source: Legit

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button