Raddi Mai Zafi ! Turawa Rarara Kudi Rashin Hankali Ne Da Wauta ~ Datti Assalafy
Na rantse da girman Allah duk wanda ya tura wa rarara tallafin kudi naira dubu daya domin ya yiwa shugaba Buhari waka sai Allah Ya tambayeshi ranar hisabi
Idan Rarara yana son shugaba Buhari tsakaninsa da Allah ba sai ya karbi kudi a hannun talakawa ba da suke fama da kuncin rayuwa, to amma abinda yayi na cewa ba zai sake yiwa shugaba Buhari wakaba har sai talakawa sun tura mishi kudi naira dubu daya’daya to wannan ya nuna ba masoyin Buhari ba ne
Rarara ai shugaba Buhari ya maka gata, ka samu arziki a gwamnatin Buhari tunda na ga har kyautar mota ka ke yi, sabani da rashin jituwar dake tsakaninka da matar shugaba Buhari Hajiya Aisha saboda tayi bikin ‘yarta Hanan bata gayyace ka ba sai ta gayyaci Hamisu Breaker bai kamata wannan ya tashi hankalinka ba indai Buharin kake so da gaske
Jama’a da ku turawa Rarara tallafin kudi naira dubu daya gwamma ku bada kudin sadaka wa mabukata shine zaku samu lada, akwai magidancin da a yanzu Naira dari gagaranshi take, Rarara yana da karfi yana da kudi, rashin hankali ne da wauta ku tura mishi kudi wai don ya yiwa shugaba Buhari waka, mu tuna da akwai hisabi, sai Allah Ya tambayemu
Allah Ya sauwake