Labarai

Duk Wanda Zai Turawa Rarara ‘Kudi Ya Tambayi Kansa Yaushe Rabonsa Da Bawa Masallacin Unguwarsu 1000 ~ Sheikh Jabir sani Mai Hula

A cewar –  sheikh jabir sani Mai hula

Fittacen malamin Addinin musulunci A jahar sokoto malamin A jami’ar Usman Dan fodiyo Dake jahar Sokoto Shekh Dr. Jabir sani Mai hula yace “Duk wanda zai turama mawaki N1,000 ya tambayi kanshi, yaushe rabonshi da bada N1,000 a Masallacin unguwarsu ko wajen tafiyar da da’awah?!

Kaima mai kushewa ka tambayi kanka, yaushe rabonka da bayarwa? Bayarwa alamu ne na so. Kada sonka ga wani ga wani yafi sonka ga Allah”

Shehin malamin yayi wanan tambihi ne A yau a shafinsa na sada zumunta na Facebook inda ya jawo hankulan Al’umma akan temakawa Addinni domin samun Rabo A duniya da lahira.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button