Labarai

Agenda 2050: Buhari ya kafa kwamitin bunƙasa Najeriya nan da shekara 30

Advertisment

Shugaban Najeriya Muhammadu ya kafa kwamitin bunƙasa ƙasar nan da shekara 30 mai suna Agenda 2050, ƙarƙashin jagorancin ɗan kasuwar nan Atedo Peterside da kuma ministar kuɗi da kasafi da tsare-tsare, Zainab Ahmed.

Ana sa ran wannan muradin na Najeriya na 2050 zai cire ‘yan ƙasar mutum miliyan 100 daga talauci sakamakon hasashen da Bankin Duniya ya yi na cewa nan da 2040 adadin ‘yan Najeriya zai kai miliyan 400.

Majiyarmu ta samu daga bbchausa kwamitin zai gaji shirin Najeriya na Vision 2020 wanda gwamnatin marigayi Umar Yar’adua ta ƙaddamar a 2009, da kuma shirin ERGP na 2017 da aka kafa domin farfaɗo da tattalin arziƙin Najeriya.

Kwamitin da gwamnatin ta kafa zai ƙunshi gwamnoni shida, ɗaya daga cikin kowane yanki na ƙasar, da kuma ‘yan majalisa da sanatoci da ministoci da wakilan hukumomi da na manyan jam’iyyu, da ‘yan kasuwa da ‘yan jarida da dai sauransu.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button