Labarai

Jinƙan Talakawa: Za Mu Dinga Sayar Da Litar Man Fetur Naira 158 Maimakon 162 Don Tausayawa Talakawa ~Cewar A.A Rano

Shugaban kamfanin gidan mai na AA Rano, Alhaji Auwalu Ali Rano ya ce duk da karin farashin man fetur zuwa naira 162 a kowace lita, kamfaninsa ba zai sayar da shi sama da naira 160 ba.

Ya ce ya yanke shawarar sayar da mai a kan naira 158 zuwa baira 160 a dukkan gidajen mansa dake fadin Nijeriya don rage wahala a tsakanin ‘yan kasa

Majiyarmu ta samu daga shafin rariya
Shugaban ya ce, duk da yadda aka yi watsi da harkar mai, wanda hakan ya haifar da gasa a tsakanin ‘yan kasuwar, amma kamfanin nasa ya yanke shawarar yin la’akari da halin da ake ciki na wahala a Nijeriya ya rage ribar da zai samu don tausayawa al’umma

Ya bayyana cewa kamfanin A.A Rano ya shirya fadada kasuwancin sa zuwa wasu bangarori kamar jiragen sama da sauran hada-hadar kasuwanci.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button