Mata ta kai mijinta kara kotu saboda ya shekara 2 ba su yi saduwar aure ba
Wata matar aure mai kimanin shekaru 25 mai suna Ruqayya Mukhtar a ranar Alhamis din nan ta shaida wa wata kotun shari’a da ke zamanta a unguwar Rigasa da ke jihar Kaduna cewa mijinta ya shafe shekara biyu bai kwanta da ita ba.
Matar wadda ta shigar da kara ta roki kotu da ta raba aurenta da mijinta mai suna Naziru Hamza, ta kuma koka kan yadda mijin ke cin zarafinta.
Sai da mijin ya musanta dukkanin zarge-zargen da ake yi masa inda ya ce yana yin iya bakin kokarinsa wajen ganin ya gamsar da matarsa a yayin saduwa.
Wani Labari: Magidanci ya saki matarsa da suka yi shekara 11 da aure saboda ta yi masa katuwa (ta yi masa ƙiba)
Inda ranka ka ji abubuwa iri-iri kamar dai yadda Wakiliya ta ci karo da sakon wata baiwar Allah da ta rubutawa malamar aji cewa:
“Salam, Malama barka da yini wallahi ina cikin gagarumin tashin hankali maza kuji tsoron haduwarku da Allah”
Matar ta cigaba da cewa
“Malama yau da safe mijina ya sakeni wai saboda nayi mishi katuwa shi ba zai iya zama da katuwar mace ba, malama yanzu 11yrs da aurenmu and we have 3kids ya rabani da yarana ya mun saki har Uku malama.”
Wakiliya ta ruwato matar na cewa abun takaici kuma a gidansa ne tayi kibar “Wallahi kafun ya Aureni bani da jiki sosai malama abun ya dameni, shin mutum shi ya halicci kanshi ne shin kiba ya zama laifi kenan”
Wallahi maza kuji tsoron gamuwarku da Allah” inji ta