Labarai

Kamfanin “Inksnation” A Mizani Na Adalci: Damfara, Ha’inci Ko Gaskiya?

Wakilan INKSNATION suna yada batanci akan Datti Assalafiy cewa an bashi kwangilar yiwa INKSNATION batanci, amma sun kasa fadin waye ya bada kwangilar, jama’a Datti Assalafiy shawara da ankararwa yakeyi, bai da ikon hana kowa ya biya kudi yayi rijista da INKSNATION, amma muna ankarar wa ne akan abinda muka bincika aka ilmantar damu akan duk wata harka na damfara da ake yinta a duniyar yanar gizo
Ga bayanin INKSNATION ta fuskar ilmin kimiyya da kuma harkokin kasuwanci na Cryptocurrency wanda zai tabbatar da cewa INKSNATION gaskiya ne ko kuma tsantsar damfarace aka shirya domin a damfari talakawan Nigeria, bani da matsala da sauran kamfanonin da suke wannan harka in banda INKSNATION
Kamar yadda wadanda suka kawo INKSNATION suke ikrarin cewa INKSNATION fasaha ce ta samun kudi wanda ya biyo hanyar fasahar kudin lantarki da ake kira “Cryptocurrency”, kamar yadda suka ce sun fito da ita ne domin fitar da mutane daga talauci
INKSNATION na dauke da tsaruka daban-daban har wajen tsaruka guda hudu, sune kamar haka:
1-BRONZE
2-SILVER
3-GOLD
4-DIAMOND
A duka wadannan tsarukan kowane tsari yafi ‘dan uwansa daraja akan abinda ake samu, ga duk wanda zaiyi rijista zai zabi tsarin da yake so cikin wadancan tsaruka guda hudun, kudin rijista ya kama daga naira dubu 1000 zuwa sama, kuma sunce a duk karshen wata zasu dinga biyan mutane ta hanyar abinda suka kira da “PinKoin”.
Kamar dai yadda suka fada; wannan Pinkoin din shine zaka canza shi ya zama farin kudi a cikin account dinka, kuma duk wanda yayi rijista dasu zai iya samun abin da ya kai sama da Naira 200,000 ba tare da yayi aikin komai ba, illa iyaka rijistan da yayi
Amma inda gizo ke sakar shine; shin INKSNATION gaskiya ne? babu yaudara da ha’inci a cikin ta?
Magana ta Gaskiya a fasahance INKSNATION bata cika dukkan ka’idojin hanyar kasuwanci da kuma fasahar Cryptocurrency ba sam-sam!
Duk wani kamfani a duniya da yake shirin shiga wannan harka bisa ka’ida dole kamfanin ya gabatar wa duniya abinda ake kira “Whitepaper”, Whitepaper takarda ce mai kunshe da tsarin kamfanonin da suke kasuwanci da kuma harkar Crytocurrency, suke bayani dalla-dalla game da fasaha da hanyoyin tabbatar da tsaron dukiyar al’umma da suka tara, da dabarun kasuwanci da sukeyi ko kuma zasuyi ga masu zuba jari ko kuma masana ilmi
Magana ta gaskiya a duk binkicen da nayi har yanzu banyi karo da Whitepaper na INKSNATION ba saboda suna da mugun nufi na guduwa da kudin mutane, kuma hatta a shafinsu na (InksNation . io) button link din da ke nuna alamar in kadannashi zaka sauke Whitepaper dinsu baya aiki kwata-kwata
INKSNATION tayi magana akan cewa tana da ‘node’ dinta, ma’ana nodes din da zasuyi yawo akan fasahar BlockChain, nuna hakan tamkar nuni da cewa ta kirkiri nata fasahar ne dai-dai da fasahar da ake kira BlockChain, duk da babu mai inkari amma kuma ta kasa gabatar da Whitepaper na wannan nodes din da take kira da InksNode, saboda basu da gaskiya
Sannan INKSNATION tana karban kudi Naira 1000 a hannun talakawa ga duk wanda zaiyi rijista, ma’ana dole ka biya daga abinda ya kama naira 1000 zuwa sama, ya danganci tsarin da ka zaba ne a lokacin rijista, wato INKSNATION sun karya ka’ida sun banbanta da sauran kamfanonin Crytocurrency, domin kuwa kowane Cryptocurrency da aka kawo kamar Bitcoin, BitcoinCash, Electorenum, Ethereum da sauransu babu wanda ya taba tambayar kudi a hannun mutane, amma INKSNATION na karba
Asalima dukkan wani sabbin fitowar wadannan kudade kyauta suke baiwa mutane ICO dinsu (Initial Coin Offering), ta hanyar abinda ake kira “Airdrop”, ma’ana zakayi rijista da su ne sannan su baka link da zaka gayyato musu mutane sai su biyaka ladan aikin ka, wannan shine gaskiya wanda babu damfara a ciki, kayi aiki a biyaka halal dinka, to amma me yasa INKSNATION zata karbi kudin mutane? muguwar babban damfara ce da ha’inci suka shirya
 
 
INKSNATION basu da sahihin gurin canja bitcoin dinsu zuwa kudi wato Exchange Market, kasancenwar Crytocurrency ba kudi bane na zahiri, dole kana bukatar kasuwar da zakaje ka canzata domin ya zame ma kudin zahiri da zakayi amfani dashi, walau ka sayar ko kuma ku canza da wani, har zuwa yanzu babu kasuwa daya na cryptocurrency da INKSNATION ya fito da ita a matsayin nanne gurun da mutane zasu je su canza kudin dan ya zame musu mai amfani
Don haka jama’a ni ban isa na hana kowa cika INKSNATION, ko matatace da ta fi kowa kusanci dani ba zan hanata ba illa iyaka na bata shawara balle kuma wani
Amma shawaran da zan baku shine duk wanda kuka san wakilin INKSNATION ne ku tabbata kun tuhumeshi duk ranar da INKSNATION suka gudu muku da kudade, ku tanadi shaidar da ta tabbatar kun basu kudin rijista wanda zaku iya gabatarwa ‘yan sanda idan lokaci yayi
Yaa Allah Ka tsare jama’ar mu daga fadawa hannun ‘yan damfara Amin
Bayyani da rubutuwa daga Shaharerren marubucin nan Datti Assalafy

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button