Kannywood

Yadda wakar Hausa ta Sambisa ta tayar da kura

Ta kaddama ta barke a kan wakar bidiyon nan ta Sambisa, wadda ke ta yawo a kafofin sada zumunta na intanet.

Takaddamar ta barke ne bayan da marubucin wakar kuma wanda ya rera ta, mai suna Sani Abdullahi Alhassan wanda aka fi sani da Sani Liyaliya Bara, ya yi korafin ba a sanya sunanasa a bidiyon wakar ba, don haka ya yi barazanar cewa ba zai kara bayar da ita a yi bidiyo ba.
“Gaskiya ne na yi korafi a kan yadda ba a sanya sunana a bidiyon wannan waka ba, saboda ni da masu shirya bidiyon mun gina abin bisa yarjejeniyar a rika sanya sunana.
“Ni ba sananne ba ne a cikin mawaka duk da na dade ina yin waka — sama da shekara 10 — saboda haka muka yi da su za su rika sanya sunana a bidiyon wakar, kuma suka amsa”, inji Sani Liyaliya.
Abubakar S Shehu, Daraktan Shirya Fina-finai da Wakokin Hausa na kamfanin 3SP da ke garin Jos, babban birnin Jihar Filato, wanda kuma shi ne ya dauki nauyin shiryawa da ba da umarnin yin bidiyon wannan waka, ya ce wannan magana haka ne sun dan samu karamin sabani da Sani Liyaliya, amma sun sasanta.

Darakta Abubakar S. Shehu (Hoto: Twitter/Kannywoodscene)

Ita dai wannan waka ta Sambisa tana cikin wakokin Hausa da miliyoyin mutane suke gani, musamman a shafin sada zumunta na YouTube.
Asalin wakar Sambisa
Da yake zantawa da wakilinmu a kan wannan takaddama, Sani Liyaliya ya ce shi ne ya kirkiri wannan waka a shekara ta 2018, kuma ya sake ta tana yawo.
Ya kara da cewa cikin ikon Allah sai wasu mutanen Jos suka ji wakar, suka ce suna so su saya, domin su yi bidiyonta – don haka suka  tattauna da su ya sayar masu da wakar, ta farko zuwa  ta uku.
Liyaliya ya kuma ce ya ba su wakar ta farko da suka yi bidiyon kuma suka sanya sunansa.
Amma matsalar da aka samu, inji shi, ita ce da ya ba su wakar ta biyu da suka yi bidiyon sai ba su sanya sunasa ba.
Ya ce da ya kira su sai suka ce ya yi hakuri sun manta ne, amma in Allah Ya yarda za su gyara a waka ta gaba.
Ya ce da ya sake ba su waka ta uku, ya tuna masu cewa kada su manta da sanya sunansa a wannan karon, suka ce ya kwantar da hankalinsa za su sanya, ba za su manta ba.
Duk da haka, a cewarsa, ya yi ta tuna masu, har sau shida zuwa bakwai a kan kada su sake mantawa wajen sanya sunansa; suka ce ya kwantar da hankalisa, amma sai ga shi da aka fitar da bidiyon, sai ya sake ganin babu sunansa a ciki.

Sani Abdullahi Alhassan wanda aka fi sani da Sani Liyaliya Bara (Hoto: YouTube/Mamaki TV)

Maganganu marasa dadi
Ganin haka, a cewar Liyaliya, ya sa “gaskiya na ji takaici”, don haka ya kira su suka yi maganganu marasa dadi.
“Wakar Sambisa wakata ce, ba su suka sanya ni na yi ba….
“Amma ba zan kara ba su wakar su yi bidiyon ta ba”, inji Liyaliya, wanda ya kara da cewa, “Tun suna karya alkawarin da muka yi da su, na daya na hakura, sun yi na biyu, to ba za a kara na uku ba.
“Dalilina ke nan na cewa ba zan kara ba su wakata su yi bidiyon ta ba”.
Ya kum
a ce gaskiya ne da yardar Allah a bidiyon wakar na gaba shi ne zai fito.
“Ina nan ina shirye-shiryen bidiyon wannan waka ta Sambisa. Bayan wannan waka kuma akwai wakokina da dama da nake son na yi bidiyonsu”, inji shi.
Inda aka samu matsala
Da yake zantawa da Aminiya, Darakta Abubakar S. Shehu ya bayyana yadda matsalar ta samo asali.
Ya ce a lokacin da suka yi bidiyon wakar Sambisa ta farko, bayan an dauki wakar an saka sunan Liyaliya a matsayinsa na wanda ya yi wakar, kuma a ka’ida haka ya kamata.
Ya kuma ce a wakar Sambisa ta biyu sai mai tace hoto ya bata masu lokaci, don haka suka yi gaggawar sakin wakar, domin sun tallata ranar da za su fitar da ita.
“Sai dai abin takaici, ashe editan bai sanya sunan mai wakar ba”, inji Abubakar.
“Bayan an saki wakar shi ne Sani Liyaliya ya kira ni, ya ce ya ga ba a sanya sunansa a bidiyon waka ba.
“Nan take na ba shi hakuri na ce in Allah Ya yarda ba za a kara ba.
“Haka lokacin da aka yi bidiyon na uku, sai aka sake samun irin wannan damuwa, wato duk wanda yake wannan harka ya san ana samun irin wadannan matsaloli, daga wajen editocin da suke tace mana ayyukanmu.
“Wallahi ban san an sake samun wannan matsala ba sai da Zainab 3SP, mai hawa wakar, ta ce ba a sanya sunan mawakin ba.
“Wallahi hankalina ya tashi, saboda ya gaya mani ya kai sau uku, cewa don Allah a sanya sunansa a bidiyon wannan waka.
“Kuma a ka’ida haka ya kamata. Na so a sanya amma ajizanci irin na dan-Adam, aka sake samun wannan matsala”, inji daraktan.
Shaharar wakar Sambisa
An dai kalli bidiyon waka ta uku ta Sambisa sau fiye da 970,000 a wata biyu da kusan rabi da suka wuce a shafin YouTibe na kamfanin 3SP.
Ranar 3 ga watan Yuli kamfanin ya wallafa ta.
Idan Sani Liyaliya ya aiwatar da barazanar da ya yi kuwa, to sababbin fuskukoki za a gani a bidiyon wakar Sambisa ta gaba. Aminiya na ruwaito 
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button