Sports

Lionel Messi: Ta faru ta kare, zakaran kwallon kafa na duniya zai bar Barcelona

Advertisment

Zakaran kwallon kafar duniya Lionel Messi ya ce zai bar Barcelona, bayan share kimanin shekara 20 yana taka leda a kungiyar.
Kungiyar ta tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na AP a ranar Talata cewa dan wasan Argentinan ya aika mata da wani bayani a rubuce da ke bayyana yunkurinsa na barin kungiyar.
Bbc na ruwaito,Wannan sanarwar na zuwa ne kwana 11 bayan ragargazar da Munich ta yi wa Barcelona da ci 8-2 a wasan daf da kusa da na karshe a gasar zakarun Turai, wanda wannan daya ne daga cikin wulakancin kwallon da dan wasan ya gani a tarihin rayuwarsa.
Messi, wanda ya lashe kyautar Ballon d’O har sau shida ya fara takawa Barce leda ne a 2004, kuma ya lashe gasar zakarun Turai har sau hudu.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button