Labarai
Covid-19: Buhari ya amince da tsawaita dokar kulle da mako huɗu
Advertisment
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake tsawaita dokar kullen da aka sassauta kashi na biyu da makonni huɗu.
Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin da shugaban ƙasa ya kafa na yaƙi da cutar korona Boss Mustapha ne ya bayyana hakan a Abuja yayin wani bayani ga ‘yan jarida kan cutar.
Wannan ne dai karo na uku da ake tsawaita kashi na biyu na sassaucin dokar kullen a faɗin ƙasar.
Advertisment
Akwai shawarwari da sakataren gwamnatin ya bai wa shugaban ƙasar kan ci gaba da sassaucin wannan doka, sai dai ba a fito da bayanai kan shawarwarin ba.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com