Labarai

Kalli Hotunan Falon Babban Attajiri A Nigeria Da Yaci Dala Amurika Miliyan Dari Biyu Amma Yanzu…….

Wannan gidan wani babban attajiri ne a Najeriya, wannan falon da zinare aka gina shi, kuma ginin wannan falon yaci kudi kimanin dalar amuruka miliya dari biyu, kudin share sharen falon kadai yana cin naira miliyan biyar a kowace wata, amma da yake duniya mayaudariya ce tuni ta yanke kauna tsakanin mai wannan daular da ni’imar daular, ta tsame shi daga wannan gidan ta kaishi wani masauki inda yake makwabtaka da miskinai, ta tsaraita shi daga tufafin alfarma sai dan tufar da bai wuce ‘yan nairori ba, sannan ta kai shi kuntatacen masauki wanda kudin gina ta bai wuce ‘yan nairori ba.
Allahu akbar ! Tun ranar da ta kaishi wannan masaukin dukiyarsa da gidansa da iyalansa suka baro shi can, babu wanda ya zauna tare da shi dan debe mishi kewa, sai wani miskini da muka raina, wanda kullum yake fuskanto mu saboda kauna mu kuma muna koransa muna hantararsa muna masa wulakanci, shi kadai ya zauna tare da shi yana debe mai kewa. Wannan miskinin shine aikin mu, shi zai muna gata ya zauna tare da mu ya rinka debe muna kewa a lokacin da danginmu gaba daya suka guje mu, alhali mun ta wulakanta shi muna kin kin kulawa da shi saboda shagala da hidimar dukiyar mu da iyalan mu. Allah swt yana cewa :
ألهكم التكاثر، حتى زرتم المقابر، كلا سوف تعلمون،
ثم كلا سوف تغلمون،
Kalli ga hotunan nan kasa wanda zaka san cewa duniya bata da tabbas.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button