Labarai

Shugaban Ukraine ya amince ya ‘tattauna da Rasha a wani wuri tsakanin Ukraine da Belarus’

 
Bayan da shugaban kasar Rasha ya cewa sojojin masu kula da makamin kare dangi Nuclear weapons su kwana cikin Shiri sai gashi kwatasam wani sabon rahoto ya samemu daga jaridar inda shugaban kasar Ukraine yake so a sasantasu.

Shugaban Ukraine ya amince ya 'tattauna da Rasha a wani wuri tsakanin Ukraine da Belarus'
President zelenskiy

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelinsky ya ce ya amince ya sasanta da Rasha a wani wuri kan iyakar Ukraine da Belarus

Mista Zelensky ya ce a tattaunawar da ya yi da shugaban Belarus Alexander Lukashenko, Ukraine ta amince ta gana da Rasha ba tare da wani sharaɗi ba a kan iyakar Ukraine da Belarus a kusa da kogin Pripyat.

Shugaban Ukraine ya ce Mista Lukashenko ya ce ya ɗauki alhakin tabbatar da dakatar da shawagin dukkanin jiragen sama, masu saukar angulu da masu kakkabo makamai mai linzame lokacin ziyarar domin tattaunawar tsakanin ɓangarorin biyu.

Tun da farko Msita Zelensky ya yi watsi da tayin Rasha na hawa teburin tattaunawa da Belarus. Ya ce ya fi buƙatar a tattauna a wata ƙasa saɓanin Belarus.

Belarus babbar aminiyar Rasha ce a yaƙin da take da Ukrainer.

Rasha ta sanar a ranar Lahadi cewa ta tura wakilai Belarus domin tattaunawa da jami’an Ukraine.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button