Kannywood
Jaruma Hauwa Ayawa Ta kafa gidauniyar Agaji
Advertisment
JARUMAR Kannywood Hauwa Abubakar Ayawa ta shiga sahun jarumai da ke da gidauniya don tallafa wa marayu, marasa ƙarfi, gajiyayyu da sauran su.
Ta kafa gidauniya mai suna ‘Hauwa Ayawa Foundation’.
Manufofin gidauniyar dai sun haɗa da taimaka wa marayu, gajiyayyu, fursunoni, majinyata, masallatai, makarantu, buɗe filin wasa don motsa jiki, taimakon yara ƙanana game da karatu, kare haƙƙin wanda aka cuta, ziyara zuwa ƙauyuka don taimako, saukar karatun Alƙur’ani duk ƙarshen wata da kuma ƙarfafa zumunci ya ɗore har gidan Aljanna.
A safiyar ranar jiya Talata, 4 ga Agusta, 2020 aka yi bikin ƙaddamar da gidauniyar a wani filin wasan yara mai suna Fantasy Park da ke Titin Swimming Pool a unguwar Shooting Range, Kabala, Kaduna.
A jawabin ta a wurin taron, Hauwa Ayawa, wadda kuma ake kira da ‘Azima Gidan Badamasi’, ta ce, “Da farko ina godiya ga dukkan mahalarta wannan wuri. Babu abin da zan ce maku sai na gode da haɗin kai da ku ka ba ni don ganin na kai ga gaci game da wannan aiki da na ɗauko.


“Ina barar addu’ar ku, domin addu’a ne kan gaba. Yau ina cikin farin ciki matuƙa, don na yi gayyata kuma an amsa gayyata na, duk da cewa ban san abin da ku ka bari ku ka zo wurin nan ba. Allah ya sa yadda mu ka taru a nan Allah ya tara mu a gidan Aljanna haka.
“Kusan dukkan waɗanda su ka halarci wannan wurin sun san abin da ya tara mu a nan. Mu na fatan Allah ya kawo mana waɗanda za su taimake mu a kan wannan manufa tamu, kuma masu tausayi.”
Bayan ta gama jawabin, an bada dama mahalarta taron su ka bada shawarwari ta yadda gidauniyar za ta cigaba da kuma ta yadda za a samu mutanen da za su rinƙa taimakawa da abin da Allah ya hore masu don cimma manufar gidauniyar.
An tashi daga taron da misalin ƙarfe 1:00 na rana,fimmagazine.com ce na ruwaito
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com