An Yankewa Dan Ta’ddan da Yakai Hari Masallacin Zealand Ya Hallaka Mutum 51 Hukuncin Daurin Rai Da Rai a Gidan Yari
Shekara guda kenan daidai bayan mummunan harin ta’addanci da wani ‘dan ta’adda mai suna Brenton Tarranta ya kaddamar a Masallacin Christchurch dake Kasar New Zealand harin da ya hallaka ‘yan uwa Musulmai 51
Yau alhamis wata kotu a Kasar New Zealand ta yankewa ‘dan ta’addan hukuncin daurin rai da rai a gidan yari ba tare da afuwa ko tara ba, zai tabbata a gidan yari har karshen rayuwarsa kafin a fitar da mushen gawarsa, zaman kotun ya gudana ne karkashin jagorancin Alkali Cameron Mander shi ya yanke hukuncin
Alkalin yace Brenton Tarrant, ya shirya sosai kafin kai harin kan wasu masallatai biyu, an sameshi da laifi, zuciyar Brenton ta kekashe, kuma bai nuna tausayi ko da na sanin abin da ya aikata ba, inji Alkali Cameron
Kamar yadda BBC Hausa ta hada rahoton, wannan dai shine karo na farko da aka yanke hukuncin daurin rai da rai ba tare da bada wata dama ba a New Zealand, kafin yake hukuncin dangin wadanda ya kashe sun bukaci kotu ta yi masa hukunci mafi tsanani
Firaministar New Zealand Jacinda Ardern, tayi murna da maraba da hukuncin da aka yankewa Brenton Tarrant, inda tace maharin ya cancanci ya karasa rayuwarsa a kurkuku, tana mai fatan daina sake jin duriyarsa har abadan abada, ta kuma yabawa dangin wadanda suka mutu saboda hakurin da suka nuna tsawon lokaci har zuwa yanzu da aka yanke hukunci.
Muna godiya wa gwamnatin Kasar New Zealand bisa tsantsar adalci da ta nunawa Musulmin duniya, sunyi kokari sosai, abubuwa da yawa na tarihi sun faru a New Zealand a sanadin harin, sun kira babban Limamin Masallacin juma’a ya karanta Qur’ani a cikin fadar majalisar dokokin Kasar, suka daukaka darajar Annabi Muhammad (SAW) da Musulmi, sannan dubbannin mutane ‘yan Kasar New Zealand sun Musulunta
Hoto: Hoton ‘dan ta’adda Brenton Tarrant, sai kuma hotunan ‘yan uwa Musulmai 51 da ya hallaka su ta hanyar harbi da bindiga
Muna rokon Allah Ya karbi shahadarsu, Allah Ya kawo karshen ta’addanci da ‘yan ta’adda a duniya Amin

![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)








