Labarai

An Je Har Gida An Kashe Ma’aurata Musulmai Tare Da Bankawa Gidansu Wuta A Kasar Amurka Amma shiru

Advertisment

Wadannan da kuke gani a hoto ma’aurata ne musulmai Jibril da Adja bakaken fata ‘yan Kasar Amurka, suna da zama a Denver Colorado Kasar Amurka.

Wasu fararen fata Amurkawa guda uku masu tsananin kin jinin Musulmai da bakaken fata
sun rufe fuskarsu da bakin kyalle suka je har gidan wadannan ma’aurata suka hallakasu sannan suka cinna wuta a gidansu

Ma’auratan sun hallaka tare da ‘ya’yan su, ta’addancin da aka musu ya faru a tun ranar 5 ga wannan wata na August amma kamar ba mutane aka kashe aka kona gidansu ba

Datti assalafy ya ruwaito,Watannin baya ‘yan sandan Amurka masu kin jinin bakin fata sun hallaka wani bakin fata George Floyd sai da aka girgiza gwamnatin Amurka a dalilin wannan kisa, har Donald Trump sai da ya bada hakuri, kuma duk duniya sai da labarin ya yadu, amma an kashe wadannan shiru, saboda Musulmai ne.

Advertisment

Musulmai mutane ne kamar kowa, suna da bukatar ayi musu adalci a matsayinsu na ‘yan adam, idan anyi zalunci akan wani da ba Musulmi ba mu kan fito mu nuna bakin ciki da alhini, amma idan aka taba Musulmi sai ayi shiru, wannan wariya ne da nuna banbancin addini.

Yaa Allah Ka karbi shahadarsu, Ka daukaka Musulunci da Musulmai. Amin.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button