Labarai

Ina shirin siyar da motata don daukar nauyin karatun saurayina, ya cancanci hakan – Budurwa

Wata budurwa ta ba ‘yan intanet mamaki ta hanyar cewa za ta siyar da motar ta domin biyawa saurayin ta kuɗin digiri na biyu wato ‘masters’. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
 

Budurwar za ta fara yi masa kasuwanci

Budurwar ta ƙara da cewa za ta yi amfani da ragowar kuɗin wajen fara wa saurayin na ta kasuwanci wanda a cewar ta ya cancanci komai.

Ina son na siyar da motata domin biyawa saurayi na kuɗin zangon ƙarshe domin ya samu ya kammala digirin sa na biyu.
A cewar Joy Turamuhawe

A yayin wata zantawa da TUKO.co.ke, Turamuhawe, ta bayyana cewa ita ta aminta da cuɗeni in cuɗeka.

Na ga mazaje da yawa waɗanda su ka yiwa ‘yan matan su abubuwa da dama saboda suna ƙaunar su, sannan ni na yarda da cuɗeni in cuɗeka. inji Turamuhawe.
 

Ina son na siyar da motata domin biyawa saurayi na kuɗin zangon ƙarshe domin ya samu ya kammala digirin sa na biyu. Ina tunanin zan yi amfani dansairan kuɗin wajen fara masa ƙaramin kasuwanci yayin da ya ke neman aiki tunda yana son yayi abinda ya karanta. Matashin sarki ya cancanci komai.

Mutane sun tofa albarkacin bakin su

Bayan ta yi wannan wallafar a shafin Twitter, ga abinda mutane ke cewa:
Joansheenah ya ce:

Cikin hawaye abin zai ƙare.

Brökë_C3lëbrïty ya ce:

Idan har da gaske ne to ina so na zama saurayin ki. Ina mamaki yadda wani ya ke ƙoƙarin neman digiri na biyu amma bai da aikin yi.

Marvin k ya ce:

Gaskiya ka da ki siyar da motar ki. Idan zai yiwu ki amshi bashi, sannan ki yi amfani da motar ki a matsayin jingina, kowane banki zai baki bashin kuɗi daganan sai ki dinga biya a hankali a hankali, saboda za ki buƙaci motarki sannan saurayin ki yayi sa’ar samun ki.





Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button