Labarai
Na damu da tsadar rayuwar da ake fuskanta – Buhari
Advertisment
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana damuwa kan tsadar kayayyakin abinci da ƴan kasar ke kuka da gwamnatinsa.
Sanarwar da mai taimakawa shugaban kan harakokin watsa labarai Malam Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce gwamnatinsa ta damu a tsadar kayayyakin a daidai lokacin kullen korona ya ƙara jefa tattalin arzikin ƙasar cikin wani hali.
Shugaban ya ce duk da matsalar ta shafi duniya baki ɗaya amma gwamnatinsa ta fara bin matakan shawo kan matsalar.
bbchausa ta kara da cewa sanarwar ta ce shugaban ya bayar da umurnin fitar da abinci kusan ton 30,000 na masara ga masu samar da abincin dabbobi domin sauƙake farashi. Ya ce yanayin da aka shiga zai zo ya wuce.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Advertisment