Kannywood

Gidan Tv Arewa24 Nishadantarwa Ko Cin Mutuncin Hausa Da Addini ? ~Indabawa Aliyu Imam

Advertisment

Duk me bibiyar shirye-shiryen wasan kwaikwayo da tashar Arewa24 ke yi zai yarda dani idan nace babu wata fa’ida ko amfanarwa da shirye-shiryen ke yi wa al’umma banda debe musu kewa.

Duk lalacewar fina-finan Hausa za ku ga  a cikinsu akan dan sami darasi ga al’umma, haka nan fina-finai na sauran kasashe, babu ma kamar kasar India wanda za ka samu fina-finansu da yawa darasi suke koyarwa don kawo gyara ga wata mummunar dabi’a ko matsala, karshen lalacewa, kasar America fina-finansu za ku ga mai gaskiya shike samun nasara, shi kuma Boss mugu a karshe yayi asara, amma banda shirye-shiryen Arewa24 irinsu Kwana Casa’in, Dadin Kowa, Gidan Badamasi, sai ka tsaya kayi ta tunanin darasin da ake koyar da al’umma a cikin shirye-shiryen amma ba zaka iya gano wa ba.

Yadda wannan tasha ta Arewa24 ta karbu a wajen mutanen arewa kusan kowanne gida ke kallonta, maimakon su dinga tsara shiri mai ma’ana da darasi, sai ake samun akasin haka, ina ma zasu yi amfani da wannan damar wajen kokarin fadakar da mutane, wayar dasu, koyar dasu darasin rayuwa, canza dabi’unsu daga mara kyau zuwa mai kyau, su yi kokarin janyo hankalin mutane wajen aikata daidai, a dinga mutunta Malam Bahaushe ana fitowa da asalin al’adarsa, da dabi’arsa ta jarumta, mazantaka da dogaro da kai, mu bamu ce dole sai sun tallata musulunci ba, mun san babban kirista ne ke juya tashar, amma su kiyaye dokokin addini da al’ada suyi wasan kwaikwayonsu mai dauke da darasi.

Maimakon haka sai su dinga tsara shirye-shiryensu suna cin mutuncin mutanen kirki, suna tozarta masu gaskiya, suna baiwa mutanen banza nasara, suna koyar da sace-sace, shaye-shaye da rashawa a fakaice, ba sa taba nuna sakamakon mai aikata wani laifi da suka nuna an aikata a shirin, su kuma dinga cin mutuncin musulunci da hausawa suna kaskantar dasu suna nuna kamar addininsu da addu’o’insu basa amfani sabanin kiristocin dake shirin, su kuma dinga cin mutuncin addini suna tozarta Alqur’ani littafi maitsarki, ta yadda suka dakko wani mutum da ake kira Nakunduba suka saka shi a matsayin Malam Nata’ala hafizin Alqur’ani mai sittin tara, ina laifi ma su sami wani mutumin kirki ko mai d’an dama-dama a saka, amma saka Nakunduba a matsayin mahaddaci Malamin addini tamkar cin fuska ne ga addini ta fuskar dabi’a.

Advertisment

Ba burina bane tozarta wannan tasha, amma wani sa’in babu yadda aka iya sai an magantu, ni bana tsoron kowa wajen fadin abinda na hakikance gaskiya ne, bani kuma da buri sama da samar da gyara a cikin al’umma, adalcin da nayi wa wannan tasha tun da farko sai da na tuntubi marubuta shirye-shiryensu har mutum guda biyu na basu shawarwari a kan wannan matsala, har nayi musu siyasa ta hanyar yabon yadda suke nuna tsarin makatantar Malam Hassan cewa hakan abu me mai matukar kyau, kamata yayi ma gwamnati ta dauki wannan tsari a kan tsangayu da makarantun Allo, bazan kama sunansu ba, amma wadan nan marubuta guda biyu in dai sun karanta wannan rubutu zasu tabbata cewa anyi haka, amma tun daga lokacin zuwa yanzu ba ta canza zani ba, ba zanyi mamaki ba watakila gidan TVn ke basu umarnin yadda labari da screenplay din shirye-shiryen zai kasance, kuma hakan ba zai zama abun mamaki ba, domin kuwa wannan gida shine ya daure gindin shirin Zafafa goma da ake na ‘bata rayuwar al’umma musamman yara a jefa su cikin aikata shaye-shaye, zinace-zinace da harkar neman maza, shirin da ake kwaikwayon mawakan kasar America masu saka d’an kunne, sarka da aikata tattoo da ass down dabi’ar masu neman maza. Hakan kuma ba zai zama abun mamaki ba domin mun ga yadda ma’aikaciyar shirin gidan ta aikata Videon batsa ya watsu a gari amma gidan sai suka ce wai babu ruwansu tunda ba’a shirin ta aikata ba, suka ci gaba da amfani da ita, salon wata ma ta sake yi.

Jama’a ku tayani alkalanci, don Allah wace irin amfana da darasi al’ummar Hausa ke amfana daga shirye-shiryen wasan kwaikwayon Arewa24? Domin ni ban gani ba, idan akwai wanda ya gani ko ya sani zai iya bayyana mana.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button