Kannywood

Aminu Saira, Falalu Dorayi, Sani Danja sun mika wuya ga hukumar tace fina-finai

Advertisment

Bayan tsawon lokaci da su ka shafe su na adawa da yin rijista ga hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a yanzu dai ta tabbata Darakta Aminu Saira da Falalu Dorayi da Sani Danja tare da Yakubu Muhammad, sun sauka daga layin da su ka dade a kan sa na nu na rashin amincewar da yin rijista da hukumar.

Labarin da mu ka samu tabbacin sa daga hukumar tace fina-finai ta jihar Kano cewa, tuni manyan ‘yan fim din su ka je suka yi rijista tare da karbar katin shaidar da ya nuna cewa su cikakkun’ yan fim ne da hukumar ta amince da su gudanar da harkokin sana’ar su bisa bin dokar hukumar tace fina-finai ta jihar Kano.

Tun a baya dai wadannan ‘yan fim din an san su da yin watsi dangane da tsarin na yin rijistar da a ka bullo da shi tun a shekarar da ta gabata, musamman ma dai Falalu Dorayi da Aminu Saira wanda sun sha shelantawa a Soshiyal Midiya cewar, yin rijistar ya saba wa doka domin haka ba za su yi ba.

Domin tabbatar da gaskiyar yin rijistar ta su wakilin mu ya ji ta bakin Aminu Saira inda ya tabbatar da yin rijistar da ya yi, sai dai bai yi wani karin bayani ba dangene da hakan.
Shi kuma shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Ismaila Na’abba Afakallahu, ya ce”Mu daman hukumar mu ba ta da matsala da kowa, abu ne dai na bin doka, kuma duk wanda ya bi doka to hukumar a shirye take ta tsare mu su hakkokin su, kuma yin rijista doka ce ta samar da ita ba wai mun kirkiro ta ba ne domin cin zarafin wani”. Inji Afakallahu.

hukumar ta kuma yi kira ga masu sana’ar fim da su mutun ta sana’ar su wajen bin doka da oda, domin ta haka ne za a samar wa da sana’ar hanyoyin ci gaba.northflix na ruwaito.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button