Kannywood

Bazan Hana ‘Ya’yana Yin Sana’ar Film Ba ~ Darakta Hassan Giggs

Guda daga cikin mai bada umarni a masana’antar fim, Hassan Giggs ya yi kira ga manyan Arewacin kasar nan da ‘yan masana’antar Kannywood da kuma al’umma su tashi tsaye wajen ciciba manhajar Northflix, sakamakon yadda manhajar ke tallafawa masana’antar Kannywood wajen kai wa ga nasarori tare da farfado da ita daga mashasharar da ta shiga.
Hassana Giggs ya bayyana hakan ne ga wakilin mu cikin zantawar da su ka yi a lokacin da ya cika shekaru 12 da auren sa. Wanda kuma ya fara da cewa.

“Sunana Hassan Giggs, kuma haifaffen jihar Kano ne ni, na yi makaranta da komai a jihar Kano, sannan zan iya cewa wannan sana’ar gadon ta na yi, domin kuwa mahaifi na mai daukar hoto ne,  kuma a wajen sa na gada, daga baya na shigo masana’antar Kannywood, duk da a gefe na ke a shekarar 1995. Daga nan cikin ikon Allah na ko yi harkokin daukar hoto mai motsi da mara matsi, a shekarar 1999/2000, har na yi fim dina na farko mai suna Saura Kiris, a nan ne na rike harkar kyamara a wannan shekarar. Na kuma kara tsunduma neman ilimi a kan fannin Daraktin a fim, kuma fim dina na farko shi ne Alkuki wanda ya fito a shekarar 2004, domin kuwa wadan da su ka taimake ni ciki akwai Ali Nuhu da Ibrahim Mandawari, saboda sun taimake ni sosai a Kannywood”.
Yanzu ‘ya’yan ku nawa da matar ka?
“Matata mun hadu da ita a shekarar 2004 a masana’antar Kannywood kamar wasa ta zo wucewa na ce ke zo, nan ta ce ya zan gayama ta haka, nan take ta ce ba za tazo ba, na fada mata cewa zan iya auran ki fa, sai ta ce a haka za ka aure ni, to bayan nan ba mu kara haduwa ba sai bayan shekara guda, Allah cikin ikon sa ban san yadda mu ka fara soyayya da ita ba, amma a shekarar 2008 watan Yuni mu ka yi aure, yanzu haka ‘ya’yan mu uku. Akwai Fatima, Aisha da kuma Nana Khadija, ina alfahari da iyali na, kuma dukan mu ‘yan fim ne, ni Darakta ita ma Darakta, amma shekaru sun ja ina da shekaru 40 da wani abun”.
Yawanci ‘yan masana’antar fim in sun yi aure ya na watsewa, amma kai gashi ku na murnar cika shekaru 12 da ita. Menene abun da ka ke gani ya zaunar da ku tare wanda su wadancan ya ke zama kamar tasgaro har zaman ya ke kasa yin dadi?
“Aure shi daman nufi ne na Ubangiji, abun da ya zaunar damu ni da mata ta shi ne, ba mu yi aure domin sha’awa ba, ba mu gina soyayya mu bisa karya ba, ba mu yi wa juna karya ba, irin a zo daga baya a na da nasani, saboda duk abun da za ka yi ba ka yi domin Allah ba, to tabbas za ka samu matsaloli, kuma duk abun da za ka yi ba wai domin ka burge jama’a ba, to babu shakka za ka zauna lafiya, idan ka yi abu domin ka burge kan ka to tabbas za ka yi kuka da kan ka. Gaskiya akwai ‘yan fim da dama wadan da su ka yi aure kuma zan iya lisafo ma su a gidajen mazajen su, mu a yanzu ido ya na kan mu saboda shahararru ne, saboda mu na fitowa duniya ta san mu, ka na yin wani abu duniya ce za ta dauka nan da nan mutane su dauka, sai ka ji mutane su na cewa au dama Giggs kai ne ka auri Muhibbat? Dama ku na tare? To sun manta cewa duk yadda Allah ya tsara rayuwar ka haka za ka tsince ta, to ‘yan fim su na zama idan ka ga aure ya mutu haka Allah ya kaddara. Duk da cewa babu wanda ya ke son hakan ta faru da shi, mu ba ma fata hakan ya faru da mu, domin mun gina auren mu bisa tsakani da Allah da gaskiya a tsakanin mu, ni na dauki mata ta a matsayin babbar abokiya ta domin ba na boye mata komai ita ma ba ta boye mun komai, duk auren da ka ga a na samun
matsala, to a na boye wasu abun a tsakanin juna, mu gaskiya mun gina auren mu bisa tsakani da Allah, shi ya sa mu ka kai shekaru 12 a yanzu”.

Ga shi matar ka a harkar fim ku ka hadu kamar yadda ka fada, akwai wani fim da ku ka shirya wanda ka ke gani matar ka za ta iya fitowa a Uwa ko Jaruma ko kuwa a wani abu, ko kuma ka fi son ta fito a cikin bayan fage kamar yadda ka ce ita ma ta na daya daga cikin ma su bada umarni a masana’antar Kannywood?
“Kamar yadda na fada maka mu yadda mu ka gina na  auren mu, ta na da ra’ayin kan ta ni ma haka, wasu abubuwan idan za ta yi sai ta nemi shawara ta ko in nemi shawarar ta, kuma ta na dara

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button