Kannywood

Duk wanda Ya Bar Tarbiyyar ‘ya’yansa a Hannun Talabijin Ba zai Ga Dai Dai Ba,Hukuncin kisa Ne Ya kamata Akan masu Fyade~ Falalu A. Dorayi

Advertisment

R A P E (F Y A D E)

Fyade dabi’a ce mummuna abar kyama da take nema ta zama ruwan dare a cikin al’ummar mu.
A fahimtar wasu mutane, dalilansu na abin da yake haifar da FYADE sunce shigar tsiraici ce.

Kashi 85% cikin 100 ayyukan FYADE da ya faru a yankunanmu, wanda muka ji da wanda muka gani da wanda muka karanta da wanda aka bani labari, ya faru ne ba tare da saka kaya masu fidda tsiraici ba.

Masu aikata wannan dabi’a zaka rasa me suke nema, domin basu kyale duk wani nau’i na mata ba. Dukkan mu mun sani masu FYADE basu kyale yarinya ba, ba su kyale tsohuwa ba, ballanta budurwa, ba su bar matan aure ba, kin bar jikinki a bude basu barki ba, Kin rufe jikinki da hijab ba su barki ba, dabiarsu Dan Akuya ma ya sallama musu wajan rashin mutunci da rashin imani.

Duk mutumin da zai afkawa yarinya yar shekara 2, 3, 4, zuwa shekara 10, 12, 13.
Ya afkawa tsuhuwa Yar shekara 50, 60, harda mai 70, wasunsu har Gawa (matacciya) indai mace ce suna afka mata, wadanda suke wannan me kuke tsammani don sun afkawa wadda take sanye da hijab.

Masu FYADE hukuncinsu shine, kawai a kashe su, KISA mai tsanani a bainar Jama’a. Domin mai irin dabi’ar ya gani ya san irin hukuncin dake jiransa shima.

Wasu da ance anwa mace FYADE sai suke fadin mai ya kaita gurin, mai FYADE baya bukatar kizo. -Kuna ina akewa Yara kanana
-Kuna ina akewa tsohuwa
-Kuna ina akewa matan aure
-Kuna ina Yanta’adda ke shiga gari su afkawa mata, su kashe mazansu.
-Kuna ina Uba ya dinga afkawa ‘Yar cikinsa daga mutuwar mahaifiyarta, Har sai da ‘Yar ta nemi agajin gaggawa.
-Kuna ina ake haura gidan mutum a saka masa bindiga a afkawa ‘yayansa mata.
-Kuna ina ake tare mutum a hanya a dauke shi da iyalansa, a kaisu jeji ai amfani da iyalansa a gaban sa, sannan ya biya kudi ya karbi kansa.
-Kuna ina ake dorawa ‘Ya talla ta nemo abin da zasu rufawa kansu asiri, a kaita KANGO ai lalata da ita da a kashe ta.
Wadannan dama wasu, duk mace ce ta kai kanta? Ko shigar tsiraici ce ta jawo?
Fasiki Fasiki ne, Idan BARGO kika rufa a jikinki a matsayin hijabi, ya keta miki haddi shine burinsa.

Na bada gaskiya ga saka hijabi ga ‘Yaya mata yana kare su daga Fituntunin zamani. Sannan mata su sani, sanya hijab umarni ne daga ALLAHU (SWT) ba fa raayi ba ne. Mafi yawan masu cewa kunfi kyau babu mayafi, ko hijab makiyanku ne, babu kaunarku ko kadan a cikin ransu, tsiraicinku ne ke birgesu, kuma baza su so suga ‘Yarsu ko Kanwarsu a haka ba.

Sannan su masu yawo tsirara, ko da kaya masu fito da surorin jiki. muddin basu tuba ba, su saurari gidan zamansu a wuta. Da tabbacin Hadisin Ma’aiki (SAW) ko kanshin Aljanna baza su ji ba.

Indai za’a kafawa wutar NEPA kwamiti domin biyar bukatar kai, yakamata ace ‘Yayan mata suna kwamitoci ba guda daya ba. Mafi yawan lokaci sakacin mu shike jefamu cikin nadama.

Mu Bawa maza ilimin Addini mu nuna musu darajar ‘Ya mace a matsayin UWA, YAYA, ‘YA, KANWA, su tashi da hakan ransu, gudun karsu tashi da Dabi’ar KARNUKA.

wasu har alfahari suke da cewa, mace in ba jininka bace maye amfaninta Wato rashin kasancewarta jini a gunsu, kamar lasisi ne na suyi duk abin da suka ga dama da ita. Gasu da ilimi amma wawaye ne, Baka da Yancin taba jikin ‘Ya mace komai rashin gatanta, kai ko a titi ta ke kwana. ba tare da yarjewar sharia ba. Shi yasa aka halatta mana aure.

Baza ka bar tarbiyar ‘Yayanka a hannu Television ba, kai tsammani zaka ga dai dai. Mafi yawan fina-finai da ake nunawa a tashohin da muke kallo, daga Films din gida har na waje, suna taka mummunar rawa wajan ruguza tarbiya.
Idan Films na gida basa nuna tsiraici na waje suna nunawa, kai harda cartoons
wanda aka fi zaunar da yara su kalla shima tuni an cusa barna a cikinsa. Idan yaro ya tashi da irin wannan kallon na tsiraici, abu mai sauki ne ya canja daga nagari zuwa mugu.

Idan Jagorori da Al’ummarsu suka zamo karkarattu, abu ne mai wahala ai hukunci na gaskiya tsakanin mutane. Mu hadu mu bada hadin kai wajan ganin duk wanda yake aikata Tabi’ar FYADE GA mata, an musu hukunci KISA. Al’umma tana cigaba ne ta hanyar hukunta duk wanda yai ba dai dai ba, musamman wadannan KARNUKAN.

Allah ya ya cigaba da tona asirin masu FYADE Ya kawo mana karshen abun.
Juma@tMbrak #sisters & #brothers

#falaluadorayi

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button