Kannywood

Farkon Kannywood, karuwai ma kyamarta suke yi – Kamaye

Sanannen marubucin nan, mai shirya fim tare da ba da umurni, Dan Azumi Baba da aka fi sani da Kamaye ya ce lokacin da aka bude masana’antar shirya fim ta Kannywood karuwai ma kyamarta suke yi.

Kamaye da aka zanta da shi a shirin Gabon Talk Show ya ce a zamanin babu macen da ke son a ga fuskarta a fim, saboda ana zaton harkar shashanci ce kawai a ciki.

Dan Azumi Baba ya ce “an yi lokacin da idan muka je gidan karuwai neman wadda za mu saka a fim, sai karuwa ‘yar’uwarta ta hana, ta ce za ki shiga fim kamar dai ‘yar iska”.

Farkon Kannywood, karuwai ma kyamarta suke yi - Kamaye
Farkon Kannywood, karuwai ma kyamarta suke yi – Kamaye

Ya ce a zamanin, Hindatu Bashir wata tsohuwar jaruma a masana’antar ce kadai ke aminta ta fito a fim.

Wani Labari na daban : Sai mun yi ‘yan dabaru muke iya biyan albashin ma’aikata – FG

Gwamnatin Nijeriya ta koka kan cewa sai ta yi ‘yan dabaru sannan take iya biyan albashin ma’aikata domin babu kudi a kasa.

Ministan kasafin kudi da tsare-tsare na kasa Atiku Bagudu ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja. Jaridar Dclhausa na ruwaito

Bagudu ya bayyana cewa kasar ta riga ta faɗa cikin wani irin matsanancin matsin tattalin arziƙi unda take fuskantar manya-manyan kalubalen ƙarancin samun kuɗaɗen shiga.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA