Labarai
Buhari ya bayar da umarnin shuka bishiyoyi miliyan 26 a arewacin Najeriya
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin shuka bishiyoyi miliyan 26.
Ya bayar da umarnin ne ga hukumar da ke kula da shuka itatuwa a yankunan da ke da barazanar kwararowar hamada.
Shugaban ya bayar da umarnin ne domin ciki alƙwarin da ya ɗauka na shuka bishiyoyin a yayin taron Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 74.
Za a shuka bishiyoyin ne a jihohi takwas na arewacin Najeriya da suka haɗa da Borno da Jigawa da Katsina da Sokoto da Yobe da Kebbi da Kano da kuma Zamfara.
Bbchausa na wallafa.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com