ALLAH BA AZZALUMIN BAWANSA BANE : Ashe Ba Abba Kyari Ba Ne Matsalar Nijeriya? ~ Daga Datti Assalafiy
Allah Ya jikan Abba Kyari tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, a lokacin rayuwarsa an zarge shi da laifin jan ragamar shugaban kasa da hana shi aikata abinda ya dace.
Bayan Allah Ya karbi rayuwarsa sai gashi har an fara cewa gwanda lokacin Abba Kyari, domin matsalolin da ake fuskanta a lokacin sa ba su kai na yanzu bayan gushewar sa ba.
Ashe dai matsalar ba na Abba Kyari bane, ina jin tsoro kar haka ta faru da shugaba Buhari, bayan ya kammala wa’adin mulkinsa ya tafi mu dawo muna cewa gwanda lokacin mulkin Buhari, kamar yadda wasu suka fara da’awar gwanda mulkin Jonathan akan na Buhari
Idan muka tuba muka gyara tsakanin mu da Allah babu shakka Allah Zai bamu mafita ta yanda bamuyi tsammani ba
Yaa Allah Ka karbi tuban mu, Ka kawo mana sauki da salama don tsarkin sunayenKa kyawawa. Amin.