Har yanzu Kano na bukatar kariya a kan Corona -Fauziya D Suleiman
Fitacciyar marubuciyar fina-finan Hausa, Fauziya D Sulaiman ta bayyana yadda sakaci da nuna halin ko in kula yake nema ya jefa jihar Kano cikin wani hali.
Marubuciyar ta bukaci gwamnati ta kawowa garin na Kano daukin gaggawa sakamakon yadda abubuwa su ke neman tabarbarewa a Kano duk da lockdown din da a kayi domin ganin an samu an dakile cutar Corona a jihar ta kano.
Fauziya D Suleiman ta bayyana hakan ne a shafin sadarwata na soshiyal midiya.
Ta ce” Ya kamata hukumomi su sa ni halin da jihar Kano ke ciki a halin yanzu, domin ya zama sai dai kawai a ce inna lillahi wa inna ilaihir raji’un,mabanbantan abubuwa sun faru ko kuma ince su na kan faruwa sakamakon kulle gari da a kayi.
Na farko da jami’an tsaron da su ke kan hanya domin kula da shige da ficen mutane, su kan su su na cikin wani hali domin basu da abun kariya, abun rufe fuska, safar hannu ko hand sanitizer, kuma an ajiye su a bakin hanya kowa yazo sai ya yi magana da su kafin ya wuce, wannan kadai ya isa ya kara yada wannan cuta da a ke gudu, tun da a wannan yanayi da suke kai za su iya cudanya da wanda ya ke dauke da cutar, sannan su hadu da wanda ba shi da cutar shi ma ya dauka ya tafi da ita. B
nan kuma sai mu’amalar da mutane su ke yi a cikin gari da kuma unguwanni, ta kai ta kawo yanzu cikin gari ya koma filin kwallo da majalisu da hira, an ce mutane su killace kan su, amma hakan taki yiwuwa, saboda mutane sun hadu waje daya sun cinkushe sakamakon hana yawo da a ka yi har gara na ce a na yawo, saboda idan a ka rabu kowa zai kama gaban sa sabanin yanzu da duk a ke cunkushe a waje guda. Abun bakin ciki na daya, wai akwai mutane da har yanzu basu yarda da wannan ciwon ba, a ce gari mai tarin ilimi kamar Kano irin wannan ta na faruwa? Bayan nan kuma akwai mace-mace da a ke yi na dattawa da yawa a jihar Kano, manyan mutane su na mutuwa sosai, dominn a ‘yan kwanakin nan an binne mutane da sunfi karfin lissafi, bai kamata a zuba ido ba, yakamata a duba a gano wannan wane irin zazzabi ne haka yake wannan kisan, sannan wani abun takaicin wai mutane su na zaman makoki”.
Marubuciyar ta kara da cewa” Ya kamata gwamnati, manyan malamai da wadanda su ke fada aji su tashi su fadakar da al’umma game da wannan cutar, domin gudun faruwar fadawa cikin wani hali, kuma ‘yan sandan da ke bakin hanya ya kamata a sama musu kayan aiki, a basu abinci a basu ruwa su na nutsu, su ma su yi aikin da a ke so su yi, sannan maganar mace-mace ya kamata a duba a bincika a ga wane irin zazzabi ne haka yake jawo mace-mace a cikin garin Kano? Bayan nan kuma har yanzu akwai mutane da su ke shige da fice a cikin garin Kano ya kamata wadanda wannan alhaki ya ke a wuyan su su duba a dakatar da su su ma, majalisu da filayen kwallo su ma yakamata a dakatar da su haka. A fadakar da al’umma abun da ya faru da kasashen da su ka ci gaba, ya kamata mu ma mu kama kan mu, sannan mu nemawa kan mu mafita”. A cewar Fauziya D Sulaiman.