Adam A Zango bai fahimci dokokin hukumar tace fina-finai ba -Afakallahu
Tun bayan da sanarwar da Adam A Zango ya sanar da cewar ya yi mubaya’a ga hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, mutane su ke ta tofa albarkacin bakin su musamman ma dai hirar da ya yi da gidan rediyon BBC, inda ya shaida cewar shi har yanzu ba dan Kannywood ba ne, kuma ya yi rajista ne a matsayin sa na jarumi mai cin gashin kan sa, sannan kuma jarumin ya bayyana cewar, hukumar a kan sa ta fara yin rijistar jarumai, kuma dokokin sa daban ne da sauran jarumai.
Dangane da hakan ne mu ka nemi karin bayani daga shugaban hukumar tace fina-finai, Isma’ila Na’abba Afakallahu, inda ya bayyana cewar “Shi Adam A Zango, sam bai ma fahimci dokokin hukumar tace fina-finai ba, domin har yanzu shi ba ya cikin wadanda su ka yi rijista da hukumar, kawai dai ya na cikin wadanda su ke neman hukumar ta yi ma sa rijista, domin kuwa a yanzu, matsayin sa shi ne wanda ya sayi fom, domin haka ya zo ya sayi Fom ya je ya cike ya dawo da shi, kuma har a ka shiga hutun Corona bai cike Fom din ba, domin haka sai ya dawo mana da fom din mun ga ya yarda da dokokin mu, sannan za mu ba shi lasisin yin aiki a matsayin sa na mai neman a yi masa rijista”.
Dangane da cewar ya yi rijista ne a matsayin sa na jarumi mai cin gashin kan sa kuwa, Afakallahu ya ce “To ai bai san dokokin hukumar ba ne shi ya sa, amma ya duba fom din da ya siya, ya ga yadda dokokin hukumar su ke, wannan duk wani abu ne da idan ya je cikewa zai gani, amma mu da ya ke bai dawo da fom din ba, to ba mu san yadda shi ya fahimci dokar ba, amma dai idan bai sa ni ba, ya kamata ya samu na kusa da shi su karanta masa domin abu ne da ya ke a rubuce cikin fom din da ya siya, sannan sai ya duba ya gani”.
Dangane da cewar shi ne a ka fara tantancewa kuwa, Afakallahu cewa ya yi “Mu a aikin mu na yin abu ne domin gyaran tarbiyya, kuma dokokin hukumar tace fina-finai, daman akwai su tun kafin na zo, kuma ba a yi su ba domin wani mutum shi kadai, abun da mu ka ce shi ne a bi su, domin haka ba za mu yarda wani ya zo ya karya doka mu zuba ido mu na kallo mu kyale shi ba. Alkawari mu ka dauka na kare mutunci da addinin mutanen jihar Kano, saboda haka idan wani ya zo zai bata su dole ne mu dauki mataki a kan sa”. Inji Afakhalla.
Afakallahu ya yi kira ga masu sana’ar fim da su fahimci cewar a na son a gyara harkokin masana’antar ne, kuma a cikin aikin gyara duk wanda ya nemi ya karya doka to doka za ta yi aiki a kansa.