Labarai

Covid19: Kwankwaso Ya Bawa Gwamnatin Kano Sabon Asibiti (Kalli Hotuna)

Advertisment

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, Ya Bada Asibiti Mai Suna “Amana Hospital” Ga Gwamnatin Jihar Kano, A Matsayin Gudummawa Don Taimakawa Kwamitin Yaki Da Annobar Cutar Covid19 A Jihar Kano.

Kamar Yadda Mai Magana Da Yawunsa A Kafafen Yada Labarai, Hon Muhd Saifullahi, Ya Bayyana, Cewa Asibitin Sabo Ne Dal, Mai Dauke Da Gadon Kwanciya Guda 60 Acikinsa, Da Sauran Kayan Aiki, Wanda A Watan Da Ya Gabata Aka Kammala Gininsa, Kazo Yanzu Ba’a Fara Aiki Dashi Ba.

Sabon Asibitin Wanda Kwankwaso Ya Gina, Ya Gina Ne Domin Taimakawa Al’ummar Jihar Kano, Musamman Talakawa, Wajen Duba Lafiyarsu Cikin Sauki. Kuma Asibitin Yana Kan Titin Miller Road, Dake Unguwar Bompai A Jihar Kano.

Kwankwasiyya Reporters Nigeria
Mon, Apr 20, 2020

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button